Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Rikakken zakin da ya tsere a Kano ya yi barna
Hukumomi a Kano sun ce rikakken zakin da ya tsere daga gidansa a gidan namun daji na jihar, ya yi barna inda ya ci awaki da jimina.
Shugaban gidan adana namun dajin na Kano Saidu Gwadabe Gwarzo ya ce Zakin ya ci awaki guda uku daga nan kuma da ya shiga bangaren jimina ya yi barna.
Ya ce duk da an ga zakin inda ya shiga amma ba a kama shi ba domin mayar da shi gidansa.
"Magungunan da aka ba shi don galabaitar da shi ba su yi masa aiki ba," in ji shi.
Tun a ranar Asabar ne rikakken zakin ya tsere daga gidansa, amma hukumomin kula da gidan adana namun dajin sun ce sun dauki matakai ta yadda ba zai iya shiga gari ba.
Idan dai har zakin ya gagara, za a iya daukar rayuwarsa wanda shi ne mataki na karshe, kamar yadda kungiyar kula da dabbobi ta duniya ta bayar da umurni a cewar Sa'idu Gwarzo.
Ya ce akwai kwararru da suka zo daga Abuja domin yi wa zakin allurar da za ta galabaitar da shi don kama shi a mayar da shi kejinsa.
Tun da farko hukumomin kula da gidan namun dajin na Kano sun ce sun yi nasarar kama zakin bayan ya shiga wani kejin awaki da suka ce sun kulle.
Amma rahotanni daga Kanon na cewa har yanzu ba a kai ga kama zakin ba.
Amma an toshe dukkanin kofofin Gidan Zoo da zakin zai iya fita ya shiga gari.
Hukumomi sun yi kira ga al'ummar Kano musamman wadanda ke makwabtaka da gidan adana namun dajin su kwantar da hankalinsu domin an dauki matakai.