Rwanda: An kashe 'yan tawayen Hutu 19

Jami'an tsaro a kasar Rwanda sun ce sun halaka "'yan ta'adda" har 19 da su ke zargi da kitsa wani hari da yayi sanadiyyar kashe mutum 14, kamar yadda 'yan sanda suka bayyana.

Rahotanni sun bayyana cewa wasu tsageru 'yan kabilar Hutu ne suka kai harin farko a ranar Juma'a a arewacin kasar.

Jami'ai a kasar sun zargi 'yan tawaye masu dauke da makamai da kai harin yayin da suka je neman kayan abinci.

Harin ramuwar gayya ya faru ne a kusa da iyakar kasar da Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo (DRC), a cewar 'yan sanda.

Me ya faru a harin na ranar Juma'a?

Wasu masu dauke da makamai ne suka fantsama dauke da wukake da gatari da duwatsu a unguwar Musanze da ke kusa da wurin shakatawa na Volcanoes National Park.

Wurin shakatawar na Volcanoes dai yana cike da baki 'yan kasasahen waje saboda kayatarsa da kuma birai da ke kai kawo a wurin.

Yayin da aka bayyana mutum takwas a matsayin wadanda suka mutu, yanzu mahukunta na cewa 14 ne suka rasun.

'Yan tawayen Hutu na Rwanda sun sha kai wa wurin shakatawar hari wadanda ke haurowa daga cikin kasar Kongo.

Wane martanin aka mayar?

'Yan sanda a Rwanda sun ce sun samu damar gano wasu daga cikin maharan.

"Jami'an tsaro sun bi sawun 'yan ta'addar, inda suka kashe 19 kuma suka kama biyar daga cikinsu," kamar yadda 'yan sanda suka bayyana.

Jami'an kula da yawon bude ido sun ce babu wanda ya samu ko kwarzane daga cikin 'yan yawon bude idon.