'David Cameroon ya yi mani karya kan ‘yan matan Chibok'

Goodluck E. Jonathan yana jawabi a wurin taro

Asalin hoton, @GEJonathan

Bayanan hoto, Goodluck Jonathan ne shugaban Najeriya a lokacin da aka sace 'yan mata daga makarantar sakandare a garin Chibok na jihar Borno

Tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Ebele Jonathan ya ce zargin da tsohon Firaministan Birtaniya David Cameron ya yi masa na cewa shi ne ya hana ceto 'yan matan Chibok "zuki ta malle ne kawai".

David Cameron, wanda shi ne Firaministan Birtaniya a lokacin da abin ya faru, ya yi zargin cewa Shugaba Goodluck Jonathan ne ya kawo wa gwamnatin Birtaniya tsaiko wajen ceto 'yan matan a lokacin da yake shugaban Najeriya.

Cameron ya yi zargin ne a wani littafi da ya wallafa mai suna For The Record.

Ya ce: "Mun hango 'yan matan na Chibok daga sama a wani kasurgumin daji....amma da alama Shugaban Najeriya (na lokacin) Goodluck Jonathan likimo yake yi kuma a karshe da ya farka sai ya zargi kungiyar rajin ceto 'yan matan da laifin siyasantar da al'amarin.

"Duk da irin muhimmancin abin, da muka bukaci mu ceto su sai ya ki ba mu hadin kai."

Wannan zargin na zuwa ne a daidai lokacin da 'yan matan na Chibok ke cika kwana 2,000 da sacewa.

Goodluck E. Jonathan yana jawabi a wurin taro

Asalin hoton, @GEJonathan

Bayanan hoto, Jonathan ya ce ya yi mamaki matuka da kalaman ganin cewa sam hakan ba ta faru ba

A martanin da ya mayar wa Mista Cameron a shafinsa na Facebook, Goodluck Jonathan ya ce ya yi mamaki matuka kan kalaman nasa, kuma ya ce ya tabbatar da cewa ba shi kadai ne yake jin cewa Cameron ya sharara karya ba.

"Ba zan zama mutum na farko ba da yake kallon wadannan kalamai a matsayin zancen kawai, sannan kuma ganin yadda mutane suke yin martani a Birtaniya ma tabbas ba zan zama na karshe ba," in ji Jonathan.

Ya kara da cewa: "Abin takaici ne Mista Cameron ya rika fadar irin wadannan abubuwa saboda duk cikinsu babu wanda ya faru.

"A matsayina na shugaban Najeriya, na rubuta wa David Cameron wasika da Barrack Obama na Amurka da kuma Shugaban Faransa François Hollande har ma da na Ira'ila Benjamin Netanyahu duka domin neman taimakonsu wajen ceto 'yan matan nan.

"Ta yaya zan nemi a taimaka mani sannan kuma na ki karbar taimakon?"

Jonathan ya kuma ce tarihi ma ya karyata Mista Cameron domin kuwa lokacin da yana Shugaban Najeriya shi ne da hannunsa ya bai wa sojojin Birtaniya damar shiga jihar Sokoto domin ceto wasu 'yan Birtaniyar da aka sace a watan Maris na 2012.

Kwana 2,000

Yau Assabar 5 ga watan Oktoban 2019 'yan matan na Chibok su 276 suke cika kwana 2,000 da sacewa daga makarantar sakandaren mata ta garin Chibok a jihar Borno.

Abin ya faru ne a daren ranar 14 ga watan Afrilun 2014.

57 daga cikinsu suka tsere daga hannun 'yan kungiyar Boko Haram, wadanda suka sace su.

Daga baya gwamnatin Muhammadu Buhari ta kubutar da sama da 100 ta hanyar tattaunawa da 'yan kungiyar, har yanzu kuma 112 suna hannunnsu.

A wata sanarwa da ta fitar a yau Asabar, kungiyar Bring Back Our Girls, wadda ke fafutikar ganin an sako su, ta ce abin takaici ne yadda aka haramta wa 'yan matan 'yancinsu na neman ilimi da ci gaban rayuwarsu.

Kungiyar ta ce cikin kaduwa da kuma nuna bacin rai ga rashin tabuka abin kirki daga bagaren gwamnatin tarayya, mata shida da aka sace daga wata makaranta a jihar Kaduna su ma sun shiga sahun na Chibok din.

"Saboda haka muna tsaye tsayin daka muna fatan samun 'yanci ga 'yan matan Chibok da duka wadanda ke hannun masu garkuwa da mutane," kungiyar ta bayyana a wani sakon da ta aike wa manema labarai.