An gano mutumin da ya shekara 17 a cikin kogo

'Yan sanda a China sun kama wani mutum da ya shiga buya tsawon shekara 17, bayan da suka yi amfani da jirgi maras matuki wajen gano wani kogo da mutumin ya boye a ciki.

An tsare mutumin mai shekara 63 wanda 'yan sanda suka sa wa suna Song Jiang ne bayan da aka kama shi da laifin safarar mata da kananan yara amma ya tsere daga gidan kaso a shekarar 2002.

Ashe duk tsawon shekarun nan, yana boye ne a wani karamin kogo.

'Yan sandan sun ce sun ga wasu alamomi da ke nuni ga mafakar Song ne a farkon watan Satumba.

Alamomin sun kai su ga wasu tsaunuka a bayan garinsu Song a lardin Yunnan a kudu maso yammacin China.

Jiragen sun gano rufin kogon mai launin shudi a jikin wani tsauni tare da wasu kayayyakin aikin gida na yau da kullum.

Daga nan ne 'yan sanda suka kai sammae wurin da kafa kuma suka gano Song a dan karamin kogo inda ya yi shekara da shekaru yana boyewa.

A cewar 'yan sanda, mutumin ya dade yana rayuwa shi kadai tsawon shekaru don haka magana da 'yan sandan ta yi masa wahala.

Kafar yada labaran jihar ta ce Song ya yi amfani da robobin ruwa wajen samun ruwan sha daga wani rafi, da kuma amfani da rassan bishiya wajen hada wuta.

A halin yanzu an mayar da shi gidan yari.