Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mota cike da mutane ta fada tekun Indiya a Mombasa
Ana fargabar wasu mutum uku da ke cikin wata mota sun halaka bayan da motar da suke ciki ta sudado daga cikin wani karamin jirgin ruwa ta fada cikin teku.
Lamarin ya auku ne da sanyin safiyar Litinin a birnin Mombasa da ke gabashin kasar Kenya.
Hadarin ya auku ne yayin da aka kai tsakiyar mashigar teku a yankin Mombasa zuwa Likoni.
An wallafa wani bidiyon abin da ya faru a shafin Twitter:
Wani wanda ya shaida abin da ya faru ya sanar da jaridar Daily Nation cewa wata mata da karamin yaro na cikin motar:
"Na ga matar da yaron a cikin motar. Ta fara kururuwa tana neman taimako lokacin da motar ta fara zamewa da baya. Na jefa musu wata igiya."
Hukumomi a kamfanin Kenya Ferry mai jirgin ruwan sun ce ana can ana neman mutanen da ke cikin motar.