Ko kun san 'illar' da man bilicin ke yi wa koda da hanta?

An yi gargadi da a kiyayi mayukan bilicin ko kuma kara hasken fata da ke sauya fata tamkar sinadarin goge fenti.

Kungiyar kananan hukumomi da ke Ingila ce ta yi wannan gargadin inda ta ce duk yadda za a yi, to lallai a yi kokarin kiyayar irin wadannan mayukan.

An bayyana cewa a kwanakin baya, jami'an da ke sa ido kan ingancin kayayyaki a Ingila sun kwace irin wadannan mayukan daga hannun diloli da masu sayar da su sakamakon rashin ingancinsu.

Kungiyar ta bayyana cewa da yawa daga cikin nau'in mayukan na dauke da sinadarin hydroquinone da kuma sindarin mercury.

Haka zalika kungiyar ''British Skin Foundation'' wacce kungiya ce a Birtaniya da ke bincike kan cututtuka irin na fatar jiki, ta bayar da shawara ga jama'a da su rinka kokarin tattaunawa da likita idan suna da wata matsala da fatar jikinsu.

Kungiyar kananan hukumomi ta Birtaniyar ta bayyana cewa masu sayar da irin wadannan mayukan na bilicin ko kara hasken fata na tallan su ne a shafukan intanet, wasu kuma na dakon su a bayan mota.

An kuma bayyana cewa kamfanonin da suke hada irin wadannan mayukan ba su fadin gaskiya dangane da kayan hadin da mayukan suka kunsa domin masu amfani da su su sani.

Kungiyar ta kwatanta sinadarin Hydroquinone da ke cikin mayukan na bilicin tamkar sinadarin goge fenti, inda ta ce mayukan kan goge fatar sama tas, kuma hakan kan iya janyo cutar kansa ko yin illa ga hanta ko kuma koda.

Haka zalika sinadarin Mercury kan iya janyo irin wadannan matsaloli da ke barazana ga lafiyar bil' adama.

A yanzu haka dai an hana amfani da mayuka masu dauke da sinadarin hydroquinone a Ingila, sai dai idan likita ne ya ba mutum umarnin amfani da su.