Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kano: An kama wanda ya halaka miji da mata da 'yarsu
Rundunar 'yan sanda ta jihar Kano ta ce ta kama wanda ake zargi da kone wasu iyali guda kurmus a jihar, abin da ya yi sanadiyyar mutuwar mai gidan da matarsa da kuma 'yarsu mai shekara biyu.
Rundunar ta sanar da haka ne ranar Asabar a wani sako da ta wallafa a shafinta na Facebook, inda ta ce rundunar musamman ce ta Puff-Adder ta cafke Salisu Idris mai shekaru 25.
A ranar Alhamis ne dai rundunar ta tabbatar da mutuwar Aminu Bala da matarsa Ruqayya Bala mai shekaru 30 da kuma 'yarsu Aisha Bala 'yar shekara biyu da haihuwa.
'Yan sanda a jihar ta Kano sun ce sun samu kiran waya ne a safiyar Laraba daga wani mutum Malam Mudassir Abdullahi da misalin karfe 3:57 na safiya, cewa gobara na ci a gidan marigayin da ke unguwar Gayawa ta karamar hukumar Ungoggo.
"Jim kadan bayan faruwar hakan jami'an rundunar suka baza komarsu domin kama wanda ake zargi, inda suka yi nasarar cafke Salisu Idris a maboyarsa da ke karamar hukumar Minjibir ta jihar Kano tare da raunuka a jikinsa," inji rundunar ta bayyana.
Ta kara da cewa: "Nan take wanda ake zargin ya amsa laifinsa sannan ya bayyana cewa ya hada kai da wani mutum guda domin cinna wa gidan wuta bayan mutumin ya yi masa alakawarin N200,000."
Rundunar ta ce ba ta kai ga kama abokin burmin nasa ba tukunna amma tana da tabbacin "ba zai tsallake komarta ba".
Ta kuma yi kira ga jama'ar gari da su ci gaba da ba ta hadin kai domin ci gaba da kiyaye rayuka da dukiyoyin al'umma a jihar.
A ranar Alhamis ma rundunar 'yan sandan Najeriya ta ce jami'anta sun ceto kusan mutum 500 a wani gini da ake tsare da su a birnin Kaduna.
Baki dayan mutanen dai maza ne, manya da yara, inda wasu ke daure da mari ko kuma sarka.