Yara na yin kicibis da hotunan batsa a intanet

Yara, har da 'yan kasa da shekara bakwai na cin karo da hotuna da bidiyon batsa a shafukan intanet, a cewar wani rahoto.

Binciken, wanda Hukumar Tace Fina-finai ta Burtaniya (BBFC) ta gudanar ya nuna cewa kashi uku cikin hudu na iyaye na ganin cewa dansu bai taba ganin hotunan batsa a kan intanet ba, sai dai sama da rabin yara sun taba gani.

Kananan yara 'yan kasa da shekara 10 sun bayyana jin kyama da kidimewa bayan ganin hotunan.

Burtaniya na kokarin toshe hanyoyin da yara za su iya ganin irin wadannan hotunan.

An bullo da wani shiri na tantance shekaru, inda za a bukaci shafukan intanet da ke samar da hotuna da bidiyon batsa su hana mutane shiga shafukan har sai in za su iya tabbatar da cewa sun haura shekara 18.

Duk lokacin da wani adireshin intanet a Burtaniya ya yi kokarin ziyartar shafin intanet da ke nuna hotunan batsa, za a bukaci mai amfani da shafin ya tabbatar da shekarunsa.

An so a fitar da sabon tsarin a watan Yuli amma an kara wata shida nan gaba.

An sanar da hukumar BBCF a matsayin mai sa ido kan tantance shekarun kuma za ta sa ido kan shafukan da ke samar da hotunan batsa don tabbatar da cewa an tantance shekarun masu ziyartar shafukan.

David Austin, shugaban hukumar BBCF ya ce: "A yanzu, hotuna da bidiyon batsa na kara samuwa ga yara a Burtaniya, kuma wannan binciken ya kara tabbatar da shaidun da muke da su na cewa hotunan batsa na yin tasiri a fahimtar yara kan jima'i, amincewa da jima'i da yadda suke kallon jikinsu.

"Binciken kuma ya nuna cewa a lokacin da kananan yara suka fara ganin irin wadannan hotuna a intanet, ba da gangan suke budewa ba."

Rahoton kuma ya duba tasirin hotunan batsa kan kanan yara. Sama da kashi 40 cikin dari na yara da suka san hotunan batsa sun amince kallon hotunan da bidiyon na sa mutane su rage girmama jinsin da ba nasu ba.

Wasu dai na ganin cewa wadanda suka so kallon wadannan hotunan za su gano hanyoyin da za su bi don kallon hotunan.