An kashe wasu yara saboda sun yi bahaya a titi a Indiya

An kama wasu mutum biyu a jihar Madhya Pradesh ta Indiya kan zarginsu da dukan wasu yara biyu da har ya yi sanadin ajalinsu saboda sun yi bahaya a titi, a cewar 'yan sanda.

'Yan sandan sun ce an kai wa Roshni mai shekara 12 da Avinash mai shekara 10 hari ne a ranar Laraba yayin da suke bahaya kusa da titin wani kauye.

Iyalan yaran sun shaida wa BBC Hindi cewa ba su da bandaki a gida.

Miliyoyin 'yan Indiya da ke cikin talauci na yin bahaya ne a waje, wanda hakan ke sa mata da yara cikin hadari.

"An yi wa yaran duka ne da sanduna har suka mutu," kamar yadda wani babban dan sanda Rajesh Chandel ya shaida wa BBC Hindu.

Ya kara da cewa: "Tuni muka shigar da karar mutanen biyu da laifin kisan kai. An fara tuhumarsu."

Da safiyar ranar Laraba ne 'yan sanda suka kama mutanen biyu Rameshwar Yadav da Hakim Yadav.

Roshni da Avinash kuwa 'ya'yan 'yan uwa suke, amma a gidansu Avinash ake rikon Roshni.

Mahaifin Avinash, Manoj, ya ce a matsayinsa na lebura ba shi da halin da zai iya gina bandaki a gidansa.

Ya kuma ce ya kasa samun tallafin da gwamnati ke bai wa marasa karfi don gina bandaki.

Wani shiri na kokarin tsaftace Indiya da ake kira da Swachh Bharat Mission ko kuma Clean India na son kawo karshen bahaya da ake yi a kan titi ta hanyar samar da bandakuna a fadin kasar.

A lokacin da Firai Ministar Narendra Modi ya kaddamar da shirin a shekarar 2014, ya yi alkawarin mayar da Indiya wacce za a daina bahaya a waje nan da 2 ga watan Oktonan 2019.

Bincike ya nuna cewa ana samun karuwar gina bandakuna, sai dai rashin ruwa da rashin kula da bandukunan da rashin sauya halayya daga mutane suna kawo cikas da kuma ci gaba da yin bahayar a waje.