Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Za mu iya daukar matakin soji kan Iran'
Saudiyya ta fito fili ta gaya wa duniya cewa ba ta da wata tantama ko shakku a kan cewa Iran ce ta kai mata hare-haren a kan muhimman cibiyoyinta na mai.
Amma karamin ministan kasar na harkokin waje Adel Al Jubeir, ya ce za su jira har sai an kammala cikakken binciken da ake yi yanzu kafin su tsayar da shawarar yadda za su mayar da martanin.
Ya ce martanin da za a mayar kuwa ya hada da na diflomasiyya, da tattalin arziki da kuma na soji.
Ministan ya kara da cewa, ''kowa yana kokarin ya kauce wa yaki, kowa yana kokarin ya ga rigimar ba ta bazu ba. Saboda haka za su auna dukkanin zabin da suke da shi, daga nan za su yanke shawara a lokacin da ya dace.
Saudiyya dai na kokarin ganin ta kafa kwakkwara kuma tartibiyar hujja a kan babbar abokiyar gabar tata, Iran a kan hare-haren.
Da dama a kasar ta Saudiyyar na ganin mayar da martani na soji na daidai-wa-daida zai iya zama babban kashedi ga Iran din.
Sai dai kuma bangaren Shugaba Trump, da ya kira hare-haren na wannan wata takalar yaki, na kokarin kauce wa shiga wani yaki.
An ruwaito Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo, yana zargin Iran da kokarin haddasa rikici da zaman gaba.
Amma a taron Majalisar Dinkin Duniya a New York, Mista Pompeo ya jaddada cewa gwamnatin Amurka na son ganin an kawo karshen kallon hadarin-kajin da kasashen biyu.
Ya ce, ''muna son sasantawa da Jamhuriyar Musulunci ta Iran. Muna fatan cimma hakan. A karshe, zai rage ga Iraniyawan su yanke shawarar hakan, ko kuma za su zabi tashin hankali da gaba.''
Ita ma Iran a nata bangaren tana kokarin ta yayyafa wa wutar da ke ta ruruwa ruwa, ta rage zaman tankiyar da ke karuwa.
A ranar Talata, Shugaba Hassan Rouhani na Iran din a wurin babban taron Majalisar Dinkin Duniya, ya gabatar da shawarar samar da wani sabon shirin tsaro a kasashen yankin Fasha.
Sai dai karamin ministan na Saudiyya kuma, Al Jubeir ya yi watsi da shawarar yana mai bayyana ta da tamkar bai wa kura ajiyar nama ne.