Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Gobara ta kashe jarirai 11 a asibiti a Aljeriya
A kalla jarirai 11 ne suka mutu yayin da gobara ta tashi da asubahin ranar Talata a wani asibiti a kasar Aljeriya.
Mai magana da yawun hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasar Captain Nassim Bernaoui, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa an ceto mata 107 daga gobarar.
Kyaftin Bernaoui ya kuma ce an ceto wasu ma'aikatan asibitin guda 30.
"Sai dai mun yi bakin cikin rasa jarirai 11 wadanda wasun su suka mutu sakamakon konewa da suka yi wasu kuma saboda hayakin da suka shaka," in ji shi.
Ba wannan ne karo na farko da aka yi gobara a bangaren 'yan haihuwa na asibitin Bachir Bennacer.
Ko a watan Mayun shekarar 2018 ma an yi gobara a wajen amma ba a samu asarar rayuka ba, a cewar kamfanin dillancin labarai na AFP.