An kama 'barayin' jarirai a Najeriya

Jarirai

Asalin hoton, Getty Images

Rundunar 'yan sandan jihar Legas a Najeriya ta bayyana rufe wani asibitin haihuwa da ke unguwar Ejigbo bisa zargin saye da sayar da jarirai.

Rufe asibitin ya faru ne bayan an zargi wata mace da satar jariri, lamarin da ya kai binciken 'yan sanda ga asibitin.

Rundunar 'yan sanda ta ce tuni ta kama mai asibitin da kuma sauran jami'an da ke aiki.

Jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan jihar Legas, DSP Bala El-Kana ya shaida wa BBC cewa wasu mata biyu ne ke sana'ar sayar da jariran.

Ya ce daya daga cikinsu malamar jinya ce kuma ita ce ta bude asibitin.

Ya ce "idan mace ta zo haihuwa sai a yaudare ta a ce mata yaronta ya mutu, sai a zaga a sayar da yaron."

Sannan ya ce wasu mata da ba su da aure kuma sun yi ciki a waje su kan kawo jariransu asibitin a ba su kudi.

"A kan sayar da jaririya mace kan naira dubu 500, jariri namiji kuwa naira miliyan guda," a cewar DSP Bala.

An kama matan biyu da jariri guda a lokacin da suka je sayar da shi, kuma an gano hotunan yara 50 a wayarsu wadanda aka sayar.

A yayin bincikensu rundunar ta gano wani jariri da aka sato daga jihar Gombe kuma aka sayar da shi a Legas wanda yanzu yake hannun 'yan sandan kuma ake kula da shi a asibiti.

DSP Bala ya ce jami'an rundunarsa na ci gaba da bincike kan lamarin.

A halin yanzu dai an rufe asibitin sannan ma'aikatansa na tsare.

Satar jarirai dai ba sabon al'amari ba ne musamman a kudu maso gabashin Najeriya, inda a shekarun baya aka sha gano wasu cibiyoyi da ake kiwon mata da ake yi wa ciki don sayar da jariransu.

Gwamnatin jihar Legas ta ce a watan Fabrairu ta ceto yara mata 100 da maza 62 a jihar kuma tuni ta damkasu ga gidajen marayu da suka yi rajista a jihar.