An tuhumi Ba'amurkiyyar da ta boye jariri a jaka da safarar yara

Jennifer Talbot

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, A ranar Alhamis ne Jennifer Talbot ta bayyana a wajen taron manema labarai

Ana zargin wata Ba'amurkiyya da laifin safarar mutane bayan samun ta da boye jariri dan kwanaki 6 a cikin jakarta, da ta ke kokarin ficewa da shi daga kasar Philippines.

A ranar Laraba ne aka cafke Jennifer Talbot, mai shekara 43, a filin jirgin sama na Ninoy Aquino International a birnin Manila.

Rahotanni sun bayyana an samu jariri dan kwanaki shida a cikin jakarta, a lokacin da ta ke kokarin hawa jirgin da zai kai ta Amurka.

Hukumomi sun zargi Miss Talbot ba ta nunawa jami'an shige da fice jaririn ba. Hukumar binciken manyan laifuka ta Philippine ta yi ikirarin matar na kokarin tserewa da jaririn ne.

Mis Talbot tare da jami'an tsaro

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Ana zatgin Mis Talbot da karya dokokin kasar Philippines da suka haramta safarar mutane

A bangare guda kuma ana tuhumar iyayen jaririn da take dokar bai wa 'yar kariya, kamar yadda hukumomi suka bayyana.

Tuni kuma aka mika jaririn gidan kula da yara.

Tun da fari Mis Talbot wadda ta fito da jihar Ohio ta Amurka, ta gagara nuna tikitin jaririn da ya halasta masa hawa jirgin.

Idan aka sameta da laifi za ta iya fuskantar daurin rai da rai, kamar yadda shugaban hukumar bincikn muggan laifuka Manuel Dimaano, ya shaidawa manema labarai.

An sanar da ofishin jakadancin Amurka a kasar halin da ake ciki.

Bayan kama ta Mis Talbot ta gabatar da wasu takardu da ta yi ikirarin sun bata damar tafiya Amurka da jaririn.

Sai dai takardun ba sa dauke da sa hannun mahaifiyar jaririn kamar yadda doka ta tanada.