Tunisia: Tsohon shugaban kasar Tunisiya Ben Ali ya mutu

Tsohon shugaban kasar Tunisiya Zine al-Abidine Ben Ali ya mutu a kasar Saudiyya, inda yake gudun hijira, kamar yadda iyalinsa suka shaida wa 'yan jarida.

Tumbuke shi da aka yi daga mulki a shekarar 2011 ta jawo juyin juya halin kasashen Larabawa.

Tshohon shugaban kasar ya shafe shekara 23 a kan mulki tare da hade kan 'yan kasar Tunisiya amma ba tare da wani 'yanci ba.

A karshe bai iya katse hanzarin masu rajin kawo sauyi a kasar ba, wadanda suka rika shirya maci, abin da ya yi sanadiyyar mulkinsa a farkon shekarar 2011.

Hakan ya tilasta masa ficewa daga kasar, abin da ya cinna wutar juyin juya hali a sauran kasashen Larabawa da ake wa lakabi da Arab Spring da Ingilishi.

Ya hau mulki a 1987 bayan ya hambarar da Habib Bourguiba domin zama shugaban kasar na biyu.