'Yan Ghana na kira ga jami'ar 'yar sanda ta yi murabus

Shugabar sashen binciken manyan laifuka ta hukumar 'yan sandan kasar Ghana, Maame Tiwaa Addo-Danquah, na cikin tsaka mai wuya, inda jama'ar kasar ke neman ta sauka daga mukaminta.

Masu kiraye-kirayen na neman jami'ar ta ajiye aiki ne bisa zargin rashin gudanar da bincike kan yadda a kashe wasu 'yan mata biyar da suka bace a bara.

Jama'ar kasar na bayyana fushinsu cewa a shekarar da ta gabata jami'ar 'yan sandan ta sanar da cewa 'yan matan na raye, kuma jami'an 'yan sanda na aiki domin ganin an dawo da 'yan matan cikin koshin lafiya.

A ranar Litinin, 'yan sanda sun sanar da cewa sakamakon binciken da suka gudanar kan kwayar halittar wasu gawarwaki da aka samu a cikin wani rami a watan jiya, ya gano cewa 'yan matan ne.

Hukumomin kasar na tsare da wasu mutum uku da ake zargi.

Iyalen 'yan matan sun bukaci a gudanar da bincike na daban kan kwayar halittar gwarwakin saboda a cewarsu ba su yarda da 'yan sandan ba.