'Ina tsoron kar saurayina ya yi wa 'ya'yana fyade yadda ya yi min'

Sarah Midgley

Asalin hoton, Sarah Midgley

Mata na ci gaba da kokawa a kasar Afirka Ta Kudu sakamakon matsalar fyade da kuma kisan gillar da ake musu a baya-bayan nan.

A kwanakin baya ne aka yi wa wata dalibar jami'a duka, lamarin da ya janyo sandiyyar rasa ranta.

Matsalar masu aikata fyade da kuma kisan wadanda ba su ji ba basu gani ba, ya sanya 'yan kasar suka gudanar da zanga-zanga a shafukan sada zumunta.

Sama da mutum 500,000 suka sanya hannu kan bukatar gwamnatin kasar da ta yi gaggawar dawo da dokar nan na daukar tsauraran matakai ga duk wanda aka samu da aikata manyan laifuka cikin har da kisa.

Shugaba Cyril Ramaphosa na kasar ya sha alwashin bullo da matakan dakile matsalolin da suka addabi kasar, ciki har da yi wa masu aikata laifi rijista ta musamman da kuma gurfanar da duk wanda aka samu da laifin aikata fyade gaban shari'a hadi da daukar tsauraran matakai a kansu.

Wata mata da ke sana'ar daukar hoto mai suna Sarah Midgley, 'yar shekaru 37 kuma mazauniyar Johannesburg ta ce har yanzu tana cikin kaduwar matsalar fyade da ta fuskanta sama da shekaru 10 da suka gabata.

Short presentational grey line

Ta ce ta dauki tsawon watanni 18 tana fuskantar cin zarafi sosai daga saurayin nata a wancan lokaci, kafin daga bisani da taga ba za ta iya lamunta ba ta rabu da shi.

A cewar ta ta sha yi masa barazanar barin sa matsawar bai sauya hali ba, sai dai a duk lokacin da ta yi yunkurin yin hakan, ya kan kara tsananta cin zarafin da yake mata.

"Yana dukana sosai, naushi ko ya shake mini wuya da kuma cizo.

"A wasu lokutan ya kan yi mini barazanar cewa zai yi wa 'ya'yana fyade kuma ya kashe su a gabana matsawar na yi yunkurin barin sa. Saboda cin zarafin har azabtar da ni yana yi da lantarki a wasu lokutan," in ji Sarah Midgley.

Protesters hold signs as they take part in a march against gender based violence and in solidarity with women who have been subject to violence and in memory of those who have been killed, at the North Beach in Durban, on September 7, 2019

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Manyan mata da 'yan mata na rayuwa cikin tsoro da fargabar kar a yi musu fyade

Ban taba tattauna matsalata da kowa ba, saboda ina jin kunyar abin da yake faruwa da ni, musamman yadda na kasa kare kaina.

Saboda irin maganganun da yake fada mini cewa 'yan uwa da abokaina babu wanda ya damu da ni ya sanya bana shiga cikin mutane. A gefe guda kuma na yi imanin cewa zai iya cin zarafin 'ya'yana.

A lokacin da na samu karfin gwiwar barinsa, na yi hakan ne a boye ba tare da kowa ya sani ba. Sai dai bayan kwanaki 10 da barin sa ne na ji sallamar sa a kofar gidana.

A lokacin na kadu sosai ta yadda ya iya gano maboyata. Sai dai ya ce mini yazo neman taimako ne a wurina.

Ya shaida mini cewa ba shi da kudi kuma yana son ya kaiwa wani kawunsa ziyara, kuma wurin na da tazarar kilomita 25 (kwatankwacin Mil 15.5 kenan) daga inda nake zaune.

A lokacin yayi mini alkawarin cewa zai fita daga rayuwata gabadaya, matsawar na taimaka masa na raka shi a mota. Kuma na yarda da shi a hakan.

Na dauki tsawon shekaru bayan na fuskanci cin zarafin, ina da na sanin cewa yadda na iya zama da shi.

horizontal line

Laifukan da suka haddasa fitna a Afirka ta Kudu tun watan Agusta.

  • Janika Mallo mai shekaru 14 wata daliba ce da ta rasa ranta sakamakon buga kan ta da aka yi jikin wani gini, lokacin da aka yi mata fyade: har yanzu babu wani mataki da aka dauka a kai.
  • Wata dalibar jami'a mai suna Uyinene Mrwetyana 'yan shekaru 19 akwai zargin cewa an tura ta wani ofishin lura da harkokin sakonni, inda aka yi mata fyade da hakan yayi sanadiyyar rasa ranta. An dai cafke wani jami'in wurin da ake zargi.
  • Itama wata dalibar jami'a Jesse Hess mai shekaru 19 an samu gawarta a kan gado da kuma kakanta Chris Lategan mai shekaru 85, da aka samu shi ma a daddaure a cikin bandaki. Kuma har yanzu babu wanda aka cafke da ake zargi da aikata hakan.
  • 'Yar wasan damben Boxing Leighandre "Baby Lee" Jengels mai shekaru 25, an samu gawarta ne a wata mota, bayan da wani tsohon saurayin ta jami'in dan sanda ya harbe ta; daga bisani ya mutu shi ma sakamakon raunin da ya samu a hatsarin mota.
  • Meghan Cremer an samu gawarta a wata makabarta daure da wata igiya a wuyanta; an gurfanar da wasu mutum uku dai da ake zargi da hannu a kisan nata
  • Ita ma Lynette Volschenk an samu gawarta ne a cikin wata jaka da aka ajiye a wani gini. Sai dai an cafke wani mutum da ake zargi nda aikata laifin.
horizontal line

Bayan mun yi 'yar tafiya me nisa ne, sai na fuskanci yanayin sa ya sauya.

Fuskar sa ta nuna yanayin fushi sosai, amma kasancewar na san ta'ammali da miyagun kwayoyi ya shiga jikin sa sosai hakan be sanya nayi tunanin wani abu ba. (Abin takaicin shine na gano yana shan kayayyakin maye ne lokacin da soyayyar mu tayi nisa).

Na shaida masa cewa zan raka shi har zuwa kofar shiga harabar gidan gonar, sannan na juya zuwa gida.

Kamar na san cewa akwai wani abu da yake shirya mini, amsar da ya ba ni ita ce, za ki koma gida a lokacin da na baki umarnin yin hakan- inda ya yi gaggawar kulle kofofin motar.

Lokacin da muka isa wurin, sai ganin sa na yi ya bude kofar motar inda ya fito da ni waje, nan take ya fara sakar mini naushi tare da buga mini wani abu a kaina lamarin da ya sanya na suma.

Lokacin da na farfado, sai na fuskanci ina daya daga cikin dakunan gidan gonar yana kokarin amfani da ni tare da wani abokinsa.

A lokacin hankalina ya sake gushewa saboda tsananin wuya, amma lokacin da na farfado sai na fuskanci ina tare da wata ma'aikaciyar gidan gonar zaune kusa da ni.

'Dole ta sa aka cire mini mahaifa'

Tana dauke da bokitin ruwa yayinda take kokarin goge mini jiki da kuma sanya mini sutura. Sai na tambayeta ta dakata ta kuma kira jami'an 'yan sanda ko kuma motar daukar marasa lafiya.

Daga bisani motar daukar marasa lafiya ta zo ta tafi da ni asibiti.

Abin takaicin shi ne raunukan da na fuskanta sakamakon cin zarafin ya sanya likitoci suka ce dole ne a cire mini mahaifa.

Bayan na sha fama da rashin lafiyar ne, nake samun labarin cewa wanda ya ci mini zarafin an bayar da belinsa har ma ya fice daga garin. Na dauki tsawon watanni tara ina waiwaye a duk lokacin da nake tafiya.

An sake cafke shi tare da yanke masa hukunci zaman gidan yari har na tsawon shekara takwas. Ya rasu sakamakon ciwon dajin mafitsara da ya sha fama da shi a shekarar 2017.

Zan iya cewa a lokacin ne na san rayuwa ta samu 'yanci bayan shekaru bakwai tana cikin kunci. Sai dai ban taba yunkurin kai wannan abokin nasa da suka ci zarafi na tare gaban shari'a ba, saboda ba zan iya jure jeka-ka-dawo ba kasancewar ina fama da kuncin cin zarafin da na fuskanta a baya.

Kusan ko da yaushe ina fama da mugayen mafarkai kan yadda tsohon saurayin nawa ya ci zarafina, har ma na fara tunani zai dawo ya ci gaba da muzguna mini tare da 'ya'yana.

Hakan ta sanya na koma gidan iyaye na, saboda ba zan iya zama ni kadai ba.

An ce idan maciji ya sare ka to ko bakin tsumma ka gani sai ka gudu.

Wannan matsala da na fuskanta a baya ta sanya nake tsoron maza. Sai dai ina kokarin boyewa, kuma ina mamakin yadda wasu mazan suke gaza gane yadda suke zama abin tsoro.

Na shiga damuwa kan yadda zan iya bai wa yarana kariya

Na dauki tsawon shekarar ina ziyartar likitan da yake ba ni shawarwari kan irin kaduwar da na fuskanta a baya, kuma wasu daga cikin su na fara fuskanta ne tun ina yarinya (Na fara fuskantar cin zarafin fyade lokacin ina yarinya karama)

Abu mafi muni shine, ga wadda ta fuskanci cin zarafin fyade a baya, kuma tana da 'ya 'ya mata guda biyu ace wadannan yaran sun fuskanci makamanciyar wannan matsala kuma.

Zan shiga dimuwa sosai idan har abun da ya faru da ni ya faru da 'ya'yana.

Saboda haka na ke shaida musu cewa zan kasance kariya a gare su, su kuma yarda da ni a ko yaushe, kofa a bude take kan duk wata matsala da ta kunno musu kuma suyi gaggawar sanar da ni.

Na shiga damuwa sosai kan yadda zan bai wa yarana kariya.

Hakan ta sanya na sayo musu wayoyin salula, sai kuma na samu kaina da sanya musu ido sosai, kuma duk inda za ni na kan fita tare da su ne suma kuma duk inda za su je na kan yi musu rakiya, ko da kuwa tare da abokansu ne.

Tens of thousands protest outside parliament against gender based violence following a week of brutal murders of young South African women in Cape Town, South Africa, 05 September 2019

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, 'Yan Afirka Ta Kudu na son gwamnati ta magance wannan ta'asa

Ina ganin babu wata doka da aka samar da za ta bai wa mata da kananan yara kariya sosai a kasar Afirka Ta Kudu.

Mutane ba sa ganin irin halin kuncin da mata ke ciki. Kuma abin takaicin shine wadanda suke daukar laifin a matsayin ba wani abu ba ne: za ka iske mata ne inda za ka ji suna cewa abin da ya faru ya riga ya faru.

Wannan ba abinda zai kawo karshen cin zarafin mata da kananan yara hadi da matsalar kisan wadanda basu ji ba su gani ba ne.

horizontal line

Yaya za'a kwatatanta Afirka ta Kudu da sauran kasashen duniya?

Daga tawagar binciken kwaf ta BBC

Zai yi wuya a kwatanta yadda matsalolin fyade ga mata ke wakana, musamman yadda kasashe ke daukar matakai kan masu aikata laifukan a bangarori da dama, a gefe guda kuma kididdigar tsawon shekaru da aka tattara kanyi batan batan dabo.

Haka kuma na iya faruwa saboda rashin fitar da rahoton yadda ake cin zarafin mata a wasu kasashe da dama.

Akwai wasu bayanan kisan da aka yiwa mata da kanana yara, sai dai wanda aka fi fitarwa shine daga sekarar 2016 zuwa yanzu.

Alkaluman hukumar lafiya ta duniya WHO sun nuna cewa kasar Afirka ta Kudu itace ta hudu a duniya da ke dauke da yawan matan da aka kashe ko kuma aka ci zarafin su.

Ana samun mutuwar mata da kaso 12.5 cikin 100,000 a Afirka ta Kudu. Sai dai kasashen Lesotho, Jamaica da Honduras sune kan gaba a duniya wajen fama da wannan matsalar. Idan aka kwatanta da rahoton da aka fitar kan kasashen duniya 183.

Wani rahoto da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar a shekarar 2016 kan cin zarafin da mata suka fuskanta a Afirka ta Kudu ya nuna cewa kaso daya cikin tara ne kacal aka kai gaban 'yan sanda, kuma kidiidgar bata kai na wadanda ke korafin abokan zaman su ne suka ci zarafin nasu ba.