Cikin 'yan Afirka Ta Kudu ya duri ruwa kan 'yan Boko Haram a Twitter

Asalin hoton, TWITTER/@DJFLOU_SA
'Yan kasar Afirka Ta Kudu sun bazama shafin Twitter suna mai yin shagube kan batun cewa kungiyar Boko Haram za ta shigar wa 'yan Najeriya fada a rikicin da ake yi na kin jinin baki a kasar.
Tun bayan fara kai wa 'yan kasashen waje hare-hare a farkon makon nan a Afirka ta Kudu ake ci gaba da samun wasu labaran bogi wadanda ake yadawa a kafafen sada zumunta musamman a Najeriya.
A ranar Talata wani rahoton bogi ya fita a shafukan intanet wanda ya yi ikirarin cewa kungiyar Boko Haram ta ce za ta kai wa Afirka Ta Kudu hari a matsayin martani game da yadda wasu 'yan kasar suke kai wa baki farmaki.
Sai dai binciken da muka yi dangane da wannan labarin ya gano cewa babu kamshin gaskiya game da wannan ikirari na barazanar kai harin.
Amma a ranar Alhamis sai 'yan Afirka Ta Kudun suka mayar da abin raha inda suka kirkiri wani maudu'i a shafin Twitter mai taken #BokoHaramChallenge, an kuma yi amfani da shi sau kimanin 40,000.

Asalin hoton, Twitter
Sun yi ta barkwanci tare da wallafa kalamai da hotuna har ma da bidiyo da ke nuna cewa cikinsu ya duri ruwa kan hari da wasu 'yan Najeriya suka fara fatan Boko Haram ta kai musu, wanda shi ma dai cikin barkwancin aka fara shi.

Asalin hoton, Halima Umar
Ga wasu daga cikin sakkonin da 'yan Afirka Ta Kudun suka wallafa a Twitter din:
Wata mai suna @PreciousMuthali ce ta rubuta sakon da ke sama cewa; "Zuwa ga Boko Haram, ku sani cewa Venda duniya ce mai zaman kanta, ba mu da hannu cikin duk wani abu da ke faruwa a Afirka Ta Kudu. Ku huta lafiya."
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 1
Wani Vusi Mpanza kuma cewa ya yi: "Ina hada kayana, zan bar ku lafiya, ban shirya fada da Boko Haram ba."
@Mollyboo kuwa wani bidiyo ta sa mai nuna wasu na gudu iya karfinsu:
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 2
@SIHLE_TUNA ne ya wallafa sakon kasa yana mai cewa: "Wane suna na 'yan Najeriya ne zai zama naku idan Boko Haram suka iso?"
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 3

Karshen labarin da aka sa a X, 4