Shirin ficewar Burtaniya daga Turai na kara shiga rudu

Boris Johnson

Asalin hoton, EPA

Gwamnatin Burtaniya ta roki sarauniya da ta tsawaita hutun da majalisar dokokin kasar ke yi, kwanaki kadan da ya rage wa 'yan majalissar su koma daga hutu a cikin watan Satumba.

Har wa yau, wannan kiran na zuwa ne 'yan makwanni gabanin cikar wa'adin da a ka dibe wa Burtaniyar domin fice wa daga Tarayyar Turai.

Boris Johnson ya ce Sarauniyar za ta yi jawabi bayan dakatar da Majalisar a ranar 14 ga watan Oktoba domin fito da kyawawan kudirce-kudircensa na majalisa.

Sai dai hakan na nufin lokacin da 'yan majalisar za su gabatar da kudirin hana Burtaniya fita daga Tarayyar Turai ranar 31 ga watan Oktoba zai wuce.

Kakakin Majalisar, John Bercow ya ce, hakan ya saba kundin tsarin mulki., inda kakakkin na majalisar wanda a al'adance bai cika mayar da martini ga al'amurran da su ka shafi siyasa ba, ya ci gaba da cewa,"sai dai a bayyane ya ke dalilin dakatar da majalisar shi ne domin a hana 'yan majalisar yin muhawara a kan shirin fitar Birtaniya daga Tarayyar Turai da kuma aiwatar da aikinsu na daidaita Kasa.

Ya kuma kara da cewa "laifi ne wanda ya saba tsarin Dimokradiya da kuma taka 'yancin 'yan majalisar da mutane su ka zaba domin su wakilce su.

Har wayau, kakakin majalisar ya kuma ce wannan cin zarafin Dimokradiyya ce.

Sai dai firai ministan ya ce, ba gaskiya ba ne danganta dalilinsa na bayar da shawarar dakatar da majalisar da dakatar da shirin fita daga Tarayyar Turai ba.

Boris Johnson ya kara da cewa, ba zai jira har sai bayan shirin fitar Burtaniya daga Tarayyar Turai ba kafin ya aiwatar da tsare-tsaren da za su ciyar da kasar gaba ba.

Ya jaddada cewa, yan majalisar na da isasshen lokacin yin muhawar fitar kasar, inda ya ce "Muna bukatar sabbin dokoki".

Mista Johnson ya kuma ce za su gabatar da sabbin kudurori masu muhimmanci shi ya sa sarauniya za ta yi jawabi.