Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
BBNaija: 'Yar sandar Birtaniya ta fito a shirin talabijin ba tare da izini ba
Wata 'yar sandar birnin Landan tana ci gaba da fitowa a shirin talabijin na Big Brother Naija a tashar Africa Magic duk da cewa ba ta samu amincewar yin hakan ba.
Rundunar 'yan sandan birnin Landan ta ce ta kaddamar da wani binciken kan batun a cikin gida bayan 'yar sandar mai suna Khafi Kareem ta bayyana a shirin, ba tare da "an ba ta izinin yin hakan ba".
Hedkwatar 'yan sandan birnin Landan ta ce Khafi, mai shekara 29 wadda 'yar Najeriya ce, ta karbi dogon hutu ne daga wurin aiki "bisa wani dalili na daban".
Wani da yake magana da yawunta ya ce "za ta yi magana kan batun idan lokaci ya yi."
Tashar talabijin ta Africa Magic ta ce Khafi ta shiga shirin ne "don amfanin zamantakewa".
An wallafa wani bayani a shafin tashar wanda yake cewa Khafi za ta kashe kyautar naira miliyan 30 (kimanin fan 68,000) wajen yin wani shirin tafiye-tafiye a Najeriya da wasu ayyukan agaji.
Rundunar 'yan sandan ta ce Khafi ta samu izinin tafiya dogon hutu ne amma ba a amince mata ta bayyana a shirin talabijin din ba.
"Rundunar tana sane cewa 'yar sandan ta bayyana a shirin ba tare da izini ba.
"Rundunar ta ce ba ta goyon bayan bayyanar 'yar sandar a shirin kuma ba ta wakiltar rundunar."
A karshe ta ce duk wani jami'inta da aka samu laifin saba ka'idojin aiki zai iya fuskartar hukunci.