Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ana ci gaba da fafutukar neman sakin Dadiyata
Kimanin mako guda kenan 'yan Najeriya ke ta kiraye-kirayen a sako wani matashi mai tashe a shafukan sadarwa na zamani, wanda ya yi batan dabo a makon jiya.
Kiraye-kirayen a sako Abubakar Idris, wanda aka fi sani a kafafen na sada zumunta da suna Dadiyata, sun biyo bayan zargin da jama'a suka yi na cewa jami'an tsaron farin kaya na DSS suka kama shi, saboda yadda yake sukar manufofin gwamnatin tarayya da ta jihar Kano.
To amma jami'an tsaron kasar sun ce ba su suka kama shi ba.
Shi dai Dadiyata mai bin akidar Kwankwasiyya ne wanda ke biyayya sau-da-kafa ga tsohon gwamnan jihar Kano, kuma tsohon dan Majalisar Dattawa, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso.
Shafinsa na Twitter cike yake da hotunansa sanye da jar hula, wadda ita ce babbar alamar kungiyar ta Kwankwasiyya.
Mai dakin matashin, Khadija Idris Dadiyata ta shaida wa BBC cewa abin ya faru ne a ranar Alhamis bayan karfe 1:00 na dare a gidansu da ke Barnawa a jihar Kaduna.
"Bayan ya dawo daga tafiya ne ya shigo gida yana kokarin kulle kofa sai wasu suka shigo suka far masa," in ji Khadija.
"Yana tsaka da yin waya ne kawai sai na ji kara. Ina daga labule sai na ga wasu mutum biyu suna kokawa da shi, amma ba zan iya tabbatar wa ba ko bindiga ce a hannun daya daga cikinsu."
Ta kara da cewa ba ta iya ganin fuskarsu ba, saboda haka ba za ta iya cewa ko su wane ne ba.
Wane ne ya kama shi?
Dan takarar gwamnan Kano na jam'iyyar PDP, Abba Kabir Yusuf dai ganin hukumar tsaron farin kaya ta DSS ce ta kama matashin.
Kakakin sa Sunusi Bature Dawakin Tofa ya shaidawa BBC cewa sun yi amanna cewa jami'an tsaron farin kayan ne suka kama shi.
Yace haka suka yi dangane da kama Salisu Hotoro, inda da farko suka musanta cewa su suka kama shi, amma ya ce daga baya sai suka ce za su kai shi kotu.
BBC ta yi yunkurin jin ta bakin kakakin rundunar 'yan sanda ta kasa Frank Mba, sai dai ya ce ba shi da masaniya kan labarin, kamar yadda ya bayyana ta wayar salula.
Da BBC ta tuntubi mai magana da yawun rundunar DSS sai dai ya ce a ba shi lokaci zai ba da amsa, amma har lokacin wallafa wannan labarin bai bayar da amsa ba.
Sai dai jaridar Daily Nigerian wadda ake bugawa a Intanet ta ruwaito rundunar a baya tana musanta zargin cewa Dadiyata yana hannunta.
"Babu wani mai suna Abubakar Idris Dadiyata a hannunmu. Ba mu kama shi ba kuma babu wani abu mai kama da haka da ya faru," in ji rundunar SSS ta jihar Kaduna a rahoton Daily Nigerian.
Jaridar ta kara da cewa 'yan sanda a jihar Kaduna su ma sun ce ba su da hannu a batansa.
Tun bayan batan na sa dai, an kaddamar da kiraye-kiraye da dama a kafofin sada zumunta na ganin an sako shi.