Gwamnatin Kaduna ta nemi a sanya wa Zakzaky sabbin sharudda

Gwamnatin jihar Kaduna ta shigar da bukata gaban babbar kotun jihar ta neman a sanya "wasu sharudda game da damar tafiya neman maganin" da kotun ta ba shugaban kungiyar IMN ta 'yan Shi'a Sheikh Ibrahim Zakzaky da mai dakinsa Zeenat.
A ranar Litinin ne babbar kotun jihar ta bai wa malamin da matarsa damar tafiya kasar Indiya bayan da lauyoyinsa suka gabatar da hujjoji game da tabarbarewar lafiyarsa.
Gwamnatin jihar wadda tun da farko ta kalubalanci bukatar ba shi izinin fita waje, yanzu kuma tana neman da a tabbatar da wasu sharudda da ta gindaya kafin a ba wa Zakzaky da matarsa damar fita neman magani.
Sai dai lauyan mutanen biyu Barrister Haruna Garba Magashi ya shaida wa BBC cewa za su kalubalanci matakin gwamnatin, yana mai cewa "ta yi ne domin kawo tsaiko kan tafiyar malam neman magani".
Gwamnatin ta zayyano wasu sharudda bakwai da take so a cika gabanin tafiyar malamin addinin kasar waje.
Babu karin bayanai
Ci gaba da duba FacebookBBC ba za ta dauki alhakin abubuwan da wasu shafukan daban suka wallafa ba.Karshen labarin da aka sa a Facebook
Ciki akwai bukatar gwamnatin tarayya ta samu tabbaci daga gwamnatin kasar Indiya cewa, "ba za ta amince da bukatar neman mafaka ta kowace irin siga daga wajen mutanen biyu ko wani daga gefe ba," in ji sanarwar.
Sauran sharuddan kamar yadda sanarwar da kwamishinan al'amuran cikin gidan jihar Kaduna, Samuel Aruwan ya sanya wa hannu, sun kunshi:
Ma'aikatar harkokin wajen Najeriya ta tabbatar da Sheikh Zakzaky da matarsa Zeenat sun nemi ganin likita a asibitin Medanta na Indiya, kuma su yi duk shirye-shiryen diplomasiyya tare da tsare-tsaren ganin mutanen biyu sun bi ka'idojin da aka kafa na tafiya neman lafiya.
Haka zalika sai kowannensu ya yi alkawarin cewa zai dawo Najeriya don ya ci gaba da fuskantar shari'a da zarar an sallame shi daga asibiti, kuma su ne da kansu za su biya wa kansu kudin tafiya da kudin magani da dawainiyarsu lokacin da suka je neman lafiya.
Sharadi na hudu sai kowannensu ya gabatar da fitattun mutanen da aka aminta da su guda biyu don tsaya musu, kuma daya daga ciki sai ya kasance sarki mai daraja ta daya a Najeriya da kuma wani fitaccen mutum da ke Kaduna wanda shi kuma zai yi alkawarin kawo su a duk lokacin da aka bukata. Kuma ma sai masu tsayawar sun gabatar da shaidar gida ko fuloti a cikin Kaduna.
Haka zalika wadanda ake kara sai kowannensu ya yi alkawari a rubuce kuma lauyansa ko nata sun sa hannu cewa, a lokacin da suke neman lafiyarsu a Indiya ba za su yi wani abu da kawo cikas ga shari'ar da ake yi musu ba, ko kuma zaman lafiya da tsaron Najeriya da ma dokokin Indiya ta kowacce irin siga ba.
Bugu da kari, jami'an tsaron Najeriya su yi wa Zakzaky da mai dakinsa rakiya, kuma su kasance tare da su a tsawon lokacin da ake yi musu magani a Indiya ta yadda za su dawo da su bayan an sallame su daga asibiti.
Sharadi na bakwai shi ne ofishin jakadancin Najeriya da ke Indiya sai ya fara tantance mutum, kafin ya bai wa duk wani damar ziyartar mutanen da ake kararsu lokacin da suke Indiya.











