Gwamnatin Barrow ta fara yi wa 'yan Gambia ba-zata

'Yan uwan mutanen da aka kashe a zamanin mulkin shugaban kasar Gambia, Yahya Jammeh sun bayyana damuwa kan sakin mutum uku da suke aikata kisan jama'a a zamanin gwamnatin ta Jammeh.

An dai saki mutanen wadanda ba jami'an tsaro ba ne da ake kira 'marasa imani' da ke tsare a hannun sojoji mako biyu bayan bayyana a gaban Hukumar Binciken Take Hakkin 'yan kasar TRRC.

Mutanen uku Malick Jatta da Omar Jallow da Amadou Badjie dai sun kasance a tsare a hannun sojoji tun 2017, bayan da Shugaba Adama Barrow ya samu nasarar cin zabe a watan Disambar 2016.

Gwamnatin Adama Barrow dai ta kafa hukumar TRRC domin binciken irin take hakkokin 'yan kasar da aka yi a tsawon zamanin da Yahya Jammeh ya yi yana mulki, da suka hada da kisa da azabtarwa da tsarewa da sauran su.

A lokacin zaman hukumar, makasan guda uku sun yi zargin cewa shugaba Jammeh ne ya umarce su su aikata wasu kashe-kashe da suka hada da na 2013, inda aka kashe wasu 'yan kasar masu jibi da Amurka da kuma wani dan jarida, Deyda Hydara.

A watan Janairun 2017 ne dai gwamnatin Yahya Jammeh na Gambia ta kawo karshe, bayan da aka rantsar da Shugaba Adama Barrow.

An samu kiki-kaka kafin a iya shawo kan Yahya Jammeh ya amince da kayen da ya sha a babban zaben kasar da aka gudanar a watan Disamban 2016.