Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Amurka da Saudiyya za su ci gaba da cinikin makamai
Majalisar dokokin Amurka ta kasa dakatar da cinikayyar makamai tsakanin kasar da Saudiyya wanda ya kai kudi kimanin dala biliyan 8.1.
Hakan na zuwa ne kwana daya bayan da shugaban Amurka, Donald Trump ya yi amfani da ikonsa na shugabanci wajen kawar da hukuncin da zauren majalisar dokokin kasar ya yanke wajen hana siyar da makaman.
Masu suka na fargabar cewa za a iya amfani da makaman wajen kai wa fararen hula da ke cikin rikicin Yemen hari.
Mista Trump dai ya yi gardamar cewa hana siyar da makaman zai rage karfin Amurka a tsakanin takwarorinta.
A cikin makon da ya gabata dai shugaban ya kuma jaddada cewa hana cikin ka iya bata alakar da ke tsakanin Amurka da kawayenta, bayan da ya yi watsi da hukuncin da majalisar ta dauka.
To sai wasu masu fada a ji da suka da wasu 'yan jam'iyyar Republicans sun ce ba shi da dalilin da zai yi watsi da hukuncin nasu.
A zaben da aka yi ranar litinin, wasu 'yan jam'iyyar Republican su 5 sun zabi da a yi watsi da abin da Trump ya ke so a yi, a yayin da suka goya wa takwarorinsu 'yan jam'iyyar Democrat baya da kashi 45 bisa 40. Sanatoci 15 dai sun ki shiga lamarin.
Gwamnatin Trump ta bayyana a cikin watan Mayun da ya gabata cewa za ta siyar wa Saudiyya da kuma Hadadiyar Daular Larabawa makamai.
Mr Trump ya kuma yanke dokar domin samu a aiwatar da yarjejeniyar ta siyar da makaman.
Ya ce ya yanke wannan hukuncin ne saboda barazanar da Iran ta ke yi wa kasarsa.
An dai jima ana fama da zaman dar-dar tsakanin Amurka da Iran, tun bayan da Amurka ta fice daga yarjejeniyar makaman nukiliyyan da ke tsakaninsu.