Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Amurka ta tura dakaru Saudiyya saboda barazanar Iran
Ma'aikatar tsaron Amurka ta Pentagon ta tabbatar da cewa za ta tura dakaru dari biyar zuwa Saudiyya saboda abin da ta kira barazana da ke karuwa daga yankin gabas ta tsakiya.
Ta ce matakin zai kara cusa tsoro kan abin da sakataren tsaron Amurka na riko ya kira babbar barazana.
Ma'aikatar tsaron Saudiyya ma ta tabbatar da cewa Sarki Salam ya amince da matakin, domin inganta tsaro a yankin.
Rabon da Amurka ta girke dakaru a Saudiyya tun 2003 da suka fice bayan kammala yaki a Iraqi.
Wannan na zuwa a yayin da Birtaniya ta shawarci jiragen ruwanta su kauracewa mashigin Hormus a tekun fasha bayan Iran ta kwace jiragenta na dakon mai guda biyu.
Shugaba Trump na Amurka ya sha alwashin aiki kafada da kafada da Birtaniya bayan Iran ta kwace jiragen dakon manta a tekun fasha.
Zaman dar-dar na kara karuwa a yankin tun bayan ma'aikatar tsaro ta Pentagon ta sanar da tura karin sojoji Saudiyya don kare abin da ma'aikatar ta kira takalar fadan Iran.
Rahotanni sun bayyana cewa tun kafin Iran ta kwashe jiragen dakon man Birtaniya aka samu labarin aike da tawagar dakarun na Amurka, amma ma'aikatar tsaro ta Pentagon ba ta sanar da haka a hukumance ba sai bayan afkuwar lamarin.
Pat Adamson ma'aikacin kamfanin jiragen Northern Marine ne na jirgin dakon man samfurin Stena Impero, ya ce sun fara shiga damuwa tun lokacin da sadarwa tsakaninsu da jirgin ta dauke.
A kwanakin baya ne dai Birtaniya ta kwace katafaren jirgin ruwan dakon man Iran wanda sojojinta na ruwa suka kama, wanda hakan ya haifar da zaman-tankiya tsakanin kasashen biyu.
Birtaniya ta yi zargin jirgin dakon man, kasar Syria ya nufa alhalin kuma hakan ya sabawa dokokin kasa da kasa musamman zargin take hakkin dan adam da sanya farar hula cikin mawuyacin hali da yakin da dakarun shugaba Assad ke jagoranta ya daidaita.
A baya dai shugaba Trump ya sha nanata cewa Amurka ba ta son yaki da Iran, to amma wasu sun fara tunanin anya kuwa aike da dakaru sansanin kasar da ke Saudiyya da kuma tekun fasha ba alamu ne na shirin yaki a kowanne lokaci da Amurka ke jiran Iran ta ce kule, ita kuma ta ce mata Cas ba?