Rikicin Libya: An kawar da bambanci

Gamayyar wasu kasashen yammacin duniya da kuma wasu na Larabawa, ta yi kira da a gaggauta kawo karshen rikicin da ake fafatawa na neman kama iko da babban birnin Libya, Tripoli .

A wata sanarwa ta hadin gwiwa da ba a saba gani ba, Amurka da Birtaniya da Faransa da Italiya da Masar da kuma Hadaddiyar Daular Larabawa, sun yi kira da a koma tattaunawa karkashin kulawar Majalisar Dinkin Duniya don kawo karsahen rikicin.

An fara dauki ba dadi ne kan neman kwace iko da babban birnin kasar ta Libya Tripoli ko Turabulus, tun lokacin da jagoran 'yan tawaye, Janar Khalifa Haftar ya kai hari kan birnin.

Kuma ya yi hakan ne a yunkurinsa na karbe Turabulus din daga hannun gwamnatin Libyar mai samun goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya da sauran wasu kasashe da hukumomi na duniya.

To amma bayan sama da wata uku dakarun 'yan tawayen na barin wuta, hakarsu ba ta cimma ruwa ba, sai ma dai baya da suka yi, inda suka yi tunga a baryar kudu ta bayan gari.

Amma kuma dauki ba dadin ya yi sanadiyyar halakar rayukan mutane kusan dubu daya.

Janar din dai yana samun goyon baya musamman daga gwamnatin Masar da ta Hadaddiyar daular Larabawa, wanda hakan ne ya sa lalle suke da tasiri da kuma muhimmanci wajen saka bakinsu wurin kiran da a dakatar da wannan zubar da jini.

Tashin hankali da rikicin siyasa sun balbalta kasar ta Libya tun bayan da aka hambarar da dadadden shugabanta, Muammar Gaddafi aka kuma kashe shi a shekara ta 2011.

Tun daga wannan lokaci ne aka samu bayyanar kungiyoyin sojin sa-kai gwammai.

Wasu daga cikin kungiyoyin mayakan na sa-kai daga bisani sun yi kawance da ko dai gwamnatin kasar mai samun goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya, da ke da mazauni a Tripoli kungiyar Janar Haftar, wanda ke kin jinin kungiyoyi ko mayaka masu ikirarin jihadi, wanda kuma yake da karfi a yankin gabashin kasar ta Libya.

Janar din dai ya taimaka wa Kanar Gaddafi ya kwace mulki a shekarar 1969, kafin daga baya abotarsu ta watse, har ya tsere zuwa Amurka, zaman gudun hijira.

Bai sake koma wa kasar ba, sai a 2011 bayan guguwar boren da aka yi wa Gaddafin ta kada, ya koma inda ya zama kwamandan 'yan tawaye.

A shekara ta 2015 aka yi nasarar kafa gwamnatin hadaka ta kasar bayan tattaunawa, amma har yanzu tana fafutukar tabbatar da ikonta a fadin kasar ta Libya, inda Janar Haftar ya sake zama dan tawaye.

Firaministan gwamnatin mai samun goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya Fayez al-Serraj, ya lashi takobin ganin ya kare ikon birnin fadawa hannun Janar din.

Tun a baya Mista Serraj ya ce ya yi wa Haftar tayin wasu mukamai domin a samu maslaha, a daina zubar da jini, amma dan tawayen ya nemi yi masa makarkashiya da zagon-kasa, kamar yadda ya ce.