Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Hotuna: An gano garin da ya shekara 9,000 a Isra'ila
An gano dubban kayan aiki da kayan kawa da mutum-mutumi da irin shuka da sauran kayayyaki a wani babban garo da ya yi shekara 9,000 daga zamanin da ake amfani da dutse a Isra'ila.
Masu binciken kayayyakin tarihi da ke karskashin kasa sun yi amannar cewa wajen, wanda yake kusa da Motza, kilomita 5 daga yammacin Birnin Kudus, a da birni ne da ke da mazauna 3,000.
Masu tono kayayyakin tarihi sun gano gine-ginen gidaje da dakuna da a baya aka rayu a cikinsu, da kuma wurare kamar na ibadah da sauran su.
An samu nau'in dawatsu irin na da...
... da kuma kwari da baka da ake amfani da su watakila don farauta ko yaki.
An samu kaburbura. Wannan wani mutum-mutumin saniya ne.
This figurine depicts a human head.
An kuma gano duwatsun ado kala-kala. Karantar su tasa aka gane cewa yara ake wa amfani da su, a cewar masu bincike.
Sauran kayayyakin sun hada da tsakiya.
Hukumar Adana Kayan Tarihi Ta Isra'ila ta ce gano wadannan abubuwa sun sauya fahimtar masana tarihi kan wadanda suka rayu a yankin a baya, inda a da suka yi amannar cewa mutane ba su zauna a yankin ba.
Dukkan hotunan hakkin mallakar Hukumar Adana Kayan Tarihi Ta Isra'ila