Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Me ya sa Saudiyya ke son gayyatar fitattun 'yan 'Casu' na duniya?
- Marubuci, Daga Manish Pandey
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakilin Newsbeat
Kasar Saudiyya ba wata kasa ba ce da jama'a ke zuwa domin rakashewa ta fannin nishadi to amma wani abin ban sha'awa shi ne yadda fitattun mawaka da makada ke kwarara zuwa can a yanzu haka.
Mariah Carey ce dai ta fara kafa tarihi a watan Janairu inda ta ziyarci kasar.
Daga nan ne kuma sai Nicki Minaj wadda ta yi na'am da shiga gasar 'casu' a birnin Jeddah to amma daga baya sai ta sauya ra'ayi ta fasa zuwa, inda ta tsaya domin shiga gangamin bikin nema wa mata da masu neman jinsi guda 'yanci.
A halin yanzu, yaran nan 'yan kasar Korea ta Kudu masu kidan badujala sun sanar da za su cashe a birnin Riyadh a watan Octoba.
Tambayar dai a nan ita ce me ya sa Saudiyya ke son fitattun 'yan casu na duniya cashewa a kasar?
Tattalin arziki
Yarima mai jiran gado, Mohammad bin Salman ya ce yana son yin sauye-sauye a kasar ta fuskar zamantakewa da tattalin arziki a wani bangare na ganin Saudiyyar ta tafi dai-dai da zamani da aka yi wa lakabi da Vision 2030.
Kasar Saudiyya dai ta dogara ne kan man fetir to amma kasancewar tangal-tangal din da aka samu a farashin man a kasuwar duniya ya sanya Saudiyyar tunanin dogaro da man babu tabbas.
Sakamakon bukatar kasar ta ganin an samu sauye-sauye a tattalin arzikin kasar musamman shigar masu zuba jari, Saudiyya take ta kokarin ta nuna wa duniya cewa kofofinta a bude suke ga 'yan kasuwa.
Kuma shigar fitattun masu casu cikin kasar wata hanya ce ta cimma burin Saudiyyar.
Sauya tsarin rayuwa
Wani fanni da Saudiyyar ke son ganin ya habaka shi ne na nishadantarwa.
'Yan Saudiyya da dama na shiga wasu kasashen duniya domin su kalli raye-raye da kade-kade da ma fina-finai domin tabbatar da cewa 'yan kasar sun kashe kudaden nasu a kasarsu maimakon fitar da su wata kasa, an gina gidajen kallo da katafaran rukunin shaguna inda masu casu za su rinka sauka su nishadantar a duk lokacin da aka gayyace su.
"Suna kokarin samar da hanyar da duniya za ta fahimci al'adar Saudiyya sannan ita ma Saudiyyar ta fahimci na duniyar," In ji Yasmin, mazauniyar Saudiyya mai shekara 24.
"Muna da mutane daga dukkanin sassan duniya da ke zaune a Saudiyya wadanda hakan zai sa kowa ya ji ana yi da shi ."
Wadansu daga cikin sauye-sauyen sun hada da kwaye wa mata takunkumin da aka sa musu na hana tukin mota da halartar filayen kwallo.
Fitattun 'yan casu da su ka je Saudiyya?
A watan Disamban 2017, Nelly ta yi casu a Jeddah duk da cewa maza ne kawai suka halarci bikin.
A wani shagalin da aka yi kwana uku ana rakashewa a Jeddah din fitattun mawaka irin su Jason Derulo da Enrique Iglesias da David Guetta da OneRepublic da The Black Eyed Peas, sun cashe.
A watan Janairu, Mariah Carey ta yi na ta casun tare da Sean Paul da DJ Tiesto.
Ba wai kida da waka kawai Saudiyyar take karbar bakunta ba.
An gudanar da gasar kokawa ta restilin a Saudiyya duk da cewa ba a bai wa matan masu kokawa damar shiga a dama da su ba.
Ko ana samun sauyi?
Yasmin wadda mazauniyar Saudiyya ce ta ce "tsaurin ba kamar a baya ba".
Ta ce a wurare kamar shagunan shan gahawa da gidan cin abinci "Kowa zai zauna a duk wurin da yake so ba tare da tsangwama ba."
To sai dai kungiyoyi masu kare hakkin bil'adama irin su Human Rights Watch (HRW) sun ce akwai tantama kan samun wani cikakken sauyi.
Duk da cewa an kyale matan suna tukin mota amma har yanzu akwai abubuwan da ba za su iya yi ba.
Kungiyar ta yi ikrarin cewa hukumomin Saudiyya sun tsare mata masu fafutuka da dama tun kafin kwaye takunkumin hana matan tuki a kasar.
Har yanzu mata a kasar na neman izni a wurin mazansu ko iyaye maza ko 'yan uwanta maza kafin ta yi tafiya zuwa kasar waje ko samun fasfo ko kuma zuwa asibiti har ma da aiki.
Ana samun suka kan halayyar kasar ga 'yancin masu neman jinsi guda.
Babu dai wasu rubatattun dokoki a kasar kan jinsin da mutum yake son saduwa da shi.
To sai dai alkalai na amfani da wasu tanade-tanaden addinin musulunci domin daukar mataki kan masu zina da luwadi da sauran ayyukan assha. In ji HRW.
Me jama'a ke cewa?
Ana samun cece-kuce dangane da mawakan BTS da za su yi casu a Saudiyya da aka sanar ranar Lahadi.
Wasu masoya na cewa bai kamata a saka siyasa ba cikin harkar ba, inda wasu ke cewa ya kamata a sanya wa Saudiyyar takunkumi saboda tarihin muzguna wa jama'a.
Yanzu dai abin jira a gani shi ne ko mawakan BTS za su je Saudiyyar su cashe a birnin Riyadh a watan Oktoba ko kuma su ma za su sauya ra'ayi kamar yadda Nicki Minaj ta soke.