Kalli hotunan barnar da rikicin 'yan Shi'a da 'yan sanda ya haifar

Wani dan sanda na tafiya a gefen wata mota da aka yi zargin 'yan Shi'a magoya bayan Sheikh Ibrahim Zakzaky da konawa a kusa da harabar majalisar dokokin Najeriya a Abuja, babban birnin kasar ranar 9 ga watan Yulin 2019.

Magoya bayan Elzakzaki da ke tsare sun yi taho-mu-gama da jami'an tsaro kuma mutane biyu sun rasu sannan da dama sun samu raunuka ciki har da 'yan sanda biyu kamar yadda hukumomi da shaidu suka bayyana.

'Yan kwana-kwana na kokarin kashe wutar da ke fitowa daga wata mota bayan rikici tsakanin jami'an tsaro da magoya bayan Sheikh Ibrahim Zakzaky.

Mummunar arangamar ta jikkata mutane. Wani takalmi a wurin da jini ya zuba yayin rikicin tsakanin jami'an tsaro da mabiya Ibrahim Zakzaky.

An lalata motoci da yin zane-zane a gine-gine a lokacin taho-mu-gamar. Nan wani wurin tsayuwar 'yan sanda ne da masu zanga-zangar suka yi rubuce-rubuce ranar 9 ga watan Yulin 2019.

Kungiyar Islamic Movement of Nigeria dai ta musanta zarge-zargen rundunar 'yan sanda na cewa magoya bayan Ibrahim Zakzaky sun harbi 'yan sandan uku. Wannan wata motar 'yan sanda ce da ake zargin masu zanga-zangar ne suka lalata.

Wani wurin duba motoci da aka lalata sakamaon artabu lokacin zanga-zangar sannan suka yi rubutun nuna kin jinin tsare shugabansu Ibrahim Zakzaky.