An nemi 'hallaka' angon Facebook a Kano

Asalin hoton, AFP
Matashin da ya yi aure ta shafin Facebook a Najeriya ya ce yana fargabar abin da zai iya faruwa bayan da ya yi zargin wasu sun kai masa hari tare da kuma samun sakwannin barazana ga rayuwarsa.
Matashin, wanda ya shiga hannun hukumar Hisbah a jihar Kano, ya ce wani ya kai masa farmaki, har ya raunata shi a hannu saboda batun aurensa a Facebook.
Tun lokacin da aka fara yayata maganar auren na Facebook, hukumar Shari'a a Kano ta ce auren ya saba wa addinin Musulunci kuma za ta hada gwiwa da hukumar Hisbah domin a hukunta shi da dukkan wadanda ke da hannu a cikin auren.
Matasan wadanda su hudu ake zargin cewa suna da hannu a wannan lamari na auren Facebook duka sun bayyana a hukumar. Kuma kowanne na nuna cewa ya yi nadama da abin da ya faru.
Babban Daraktan Hukumar Hisbah, Mallam Abba Saidu Sufi ya ce sun saurari matasan, kuma sun yi ma su nasihohi inda angon na Facebook da sauran abokansa suka amsa laifinsu tare da yin nadamar abin da suka aikata.
"Sun yi wasa da Sunnah ta Manzo SAW, domin harkar aure ba abar wasa ba ce, harka ce ta Sunnar Manzo SAW," in ji shi.
Ya kuma ce zuwa wani lokaci a cikin wannan makon ne, hukumar Hisba za ta yanke shawara a kan matakin da ya kamata ta dauka a kan matasan.
Hisbah ta yi Allah-wadai da barazanar da matashin ya ce wasu na yi masa, sannan ta nemi 'yan sanda su dauki mataki domin ba shi kariya.
A makon da ya wuce ne maganar auren na Facebook ta fito fili, inda wani matashi Sanusi Abdullahi da ke birin Kano ya tabbatar da cewa shi da wata budurwa mai suna Zainab da ke a Maiduguri da wasu abokansu sun hadu sun daura musu aure.
Kuma an daura auren ne bisa sadaki N20,000 wanda za a biya lokacin da amarya ta tare. Amma a cewar angon sun yi hakan ne da sunan raha ko wasa.
Wannan batun auren Facebook din dai ya haifar da muhawara a tsakanin malamai a jihar Kano.
Yayin da wasu ke cewa auren ya dauru, wasu kuma suka ce bai halatta ba.
Kuma ana haka ne hukumar Shari'a a jihar ta shiga cikin maganar tana cewa auren bai dauru ba, kuma wajibi ne a ladabtar da matasan.











