Sniper: 'Yar hidimar kasa ta mutu a garin kashe kwarkwatar kanta

Asalin hoton, AYOMIKUN JULIANA
Wata matashiya da ke yi wa kasa hidima NYSC a jihar Osun da ke kudu maso yammacin Najeriya ta mutu sakamakon amfani da maganin kwari na sniper don kashe kwarkwatar da ke kanta.
Hukumar NYSC reshen jihar ta tabbatar wa da BBC cewa Ayomikun Ademorayo ta mutu ne a ranar Lahadi.
Rahotanni sun ce ta sanya sniper din din a kanta ne don kashe kwarkwatar amma jim kadan bayan hakan sai ta fita hayyacinta.
Daga nan ne aka garzaya da ita asibiti inda ta mutu a can.
Tuni hukumar NYSC ta ce ta sanar da dangin marigayiyar batun mutuwar tata.
Kawayenta da suke hidiimar kasa tare sun ce lamarin ya faru ne a lokacin da take kokarin kwance kitson da ta yi domin yin sabo don shirin bukin zagayowar ranar haihuwarta.
Sun ce sun yi kokarin ceton ranta, amma hakarsu ba ta cimma ruwa.
Marigayiya Ademorayo dai marainiya ce da ta rasa dukka iyayenta kuma tana da kanne da take kula da su da daukar dawainiyarsu.
Ta kammala karatun digirinta a Jami'ar Tai Solarin da ke Ijebu-Ode a jihar Ogun.
Maganin kwari na Sniper yana da matukar karfi sosai, kuma a baya-bayan nan ana samun rahotanni na karuwar yadda matasa ke amfani da shi wajen kashe kansu.











