Afcon: A wane fanni kasashen da ke fafatawa suka yi zarra?

Ana ci gaba da Gasar Cin Kofin Nahiyar Afirka AFCON inda kungiyoyi 24 na kasashen nahiyar ke fafatawa.

Amma baya ga wasan kwallon, mun ga dacewar a dan yi raha da wasa kwakwalwa ta wani bangare, kamar tambayar: "Wa zai yi nasara a wasu bangarorin a AFCON baya ga kwallon kafa?

Wannan wasan namu na wasa kwakwalwa ya zakulo abubuwan da kowace kasa ta yi zarra a kai kamar saurin intanet da tsawon rai da rashin cin hanci da dai wasu muhimman batutuwan.