Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abba Kyari da Boss Mustapha: Buhari ya sake nada su a karo na biyu
Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya sake nada Abba Kyari a matsayin shugaban ma'aikata na fadarsa da kuma Boss Gida Mustapha a matsayin babban sakataren gwamnatin tarayya.
Mai bai wa shugaban shawara kan kafafen yada labarai Bashir Ahmad ne ya sanar da hakan a shafinsa na Twitter a ranar Juma'a.
Ya ce nadin nasu zai fara aiki ne daga ranar 29 ga watan Mayun 2019, wato ranar da shugaban ya sha rantsuwar karbar mulki a karo na biyu.
Wannan lamari na zuwa ne a daidai lokacin da wasu 'yan Najeriya ciki har da 'yan jam'iyyar APC ke nuna adawa da ci gaba da kasancewar Abba Kyari a matsayin shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasar.
Waiwaye
A farkon makon da ya gabata ne 'yan Najeriya suka sako gwamnatin Shugaba Buhari a gaba a shafukan sada zumunta tare da kiraye-kirayen a kori wasu na gaba-gaba a gwamnatinsa.
Mutane da dama ne suka yi ta bayyana ra'ayoyinsu a Twitter, inda suke kiran da a kori Abba Kyari shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa daga mukaminsa da kuma Mamman Daura.
Mamman Daura dan uwa ne na kusa ga shugaban - Buhari baffansa ne - kuma duk da cewa ba shi da mukami a gwamnatin amma ana hasashen cewa yana da fada-a-ji a fadar ta shugaban kasa.
Wannan ya biyo bayan wata zanga-zangar da wasu matasan jam'iyyar APC mai mulki suka yi ne a ranar Litinin domin neman shugaban da ka da ya sake nada ministocin da suka ce sun "hana ruwa gudu a wa'adinsa na farko".
Sannan kuma sun yi zargin cewa ministocin "ba sa son talaka, kuma ba su da gaskiya."
A wancan lokacin wasu sannanun mutane ma irin sy Sanata Shehu Sani ba a bar su a baya ba, inda ya tofa albarkacin bakinsa a Twitter yana cewa:
"Wannan zanga-zanga ana yi ne tsakanin 'yan tsirari masu fada-a-ji na fadar shugaban kasa da kuma gungun matasa domin neman iko a fadar gwamnati."
Wasu da dama sun saka hotunansu a wurin zanga-zangar da suka yi ta ranar Litinin suna yin zambo da ba'a da sauran kalamai iri-iri kan Abba Kyari da Shugaba Buhari da Mamman Daura.
@lifeinarewa ya ce '"Yan Najeriya ba Abba Kyari suka zaba ba, ba kuma Mamman Daura ba."
@OlayinkaLere ko cewa ya yi: "Ko da Buhari ya kai miliyan daya (saboda karfin isar mulkinsa) ba zai taba korar Abba Kyari ba."
@PaulPositive4 shagube yake yi cewa wasu suna tunanin Buhari zai kori Abba Kyari, ta yaya Buhari zai kori kansa?
Ammai mai magana da yawun shugaban, Malam Garba Shehu, ya gaya wa BBC cewa wasu masu neman mukami ne suka debo mutane domin yin zanga-zangar.
"Wasu sun sa ido kan wadannan mukamai saboda wasu bukatu nasu," in ji shi.