Wani ya makale a tayar jirgi daga Kenya zuwa London
Jami'ai a Kenya sun ce ana tunanin mutumin da ya makale a jikin jirgin Kenya Airways wanda ya fado a London ma'aikacin filin jirgin sama ne a Nairobi.
Jirgin wanda ya taso daga filin jirgin sama na babban birnin kasar Kenya zuwa filin jirgin Heathrow na Landan yana tafiya ne a yayin da gawar wani mutum ta fadi a wani lambu ranar Lahadi.
Shugaban Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Kenya ya shaida wa BBC cewa akwai yiwuwar cewa mutumin yana da hanyar shiga filin jirgin bisa ka'ida.
'Yan sandan Birtaniya sun ce za a yi gwaje-gwaje a jikin gawar.
Gawar ta fado ne daga nisan mita daya da wani gida da iyalan gidan ke shan hantsi a lambu a yankin Clampham da ke wajen gari a kudancin Landan, a cewar wani mai makwabtaka da wajen.
Mutumin wanda bai so a ambaci sunansa, ya ce ya ji fadowar wani abu "tim" don haka sai ya leka ta tagar benensa sai ya ga gawa da kuma "jini ta ko ina a jikin bango da lambun."
"Sai na fita waje, kuma a sannan ne mai makwabtaka da wajen ya fito yana karkarwa.," a cewarsa.
Makwabcin ya ce wani mutumin da ke bibiyar zirga-zirgar jirage a wata manhaja ta intanet a yankin Clapham Common ya ga lokacin da gawar ta fado.
Mai bibiyar jirage ya iso a lokaci daya da 'yan sanda ya kuma shaida musu cewa gawa ce ta fado daga jirgin Kenya Airways.
Da yake bayyana wanda ya mutu, ya ce: "Dalilin da ya sa gawar ba ta rugurguje ba shi ne saboda yadda jikin ya kankare gaba daya."

Asalin hoton, SWNS
Har yanzu ba a gano ko waye mamacin ba.
'Yan sanda sun yi amannar cewa mutumin ya fado ne daga maboyar tayoyin jirgi - inda bayan da jirgin ya sauka samu ruwa da jaka da abinci a wajen.
Shugaban Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Kenya Gilbert Kibe, ya shaida wa BBC Afirka cewa akwai tsaro sosai a filin jirgin sama na Jomo Kenyatta International da ke Nairobi.
Ya kara da cewa zai yi wahala wani da ba shi da alaka da wajen ya shiga har titin da jirgi ke tashi, ya shiga cikina ba tare da an ganshi ba.
"Suna duba ko ina na cikin jirgin har da tayoyinsa da karkashinsa. Suna duba komai. Kuma in dai har aka yi wannan binciken da wuya wani mutum ya kasance a wajen ba tare da an gans hi ba.
"To da wane lokaci ne mutumin ya samu shiga, wannan wani boyayyen lamari ne," a cewar Mista Kibe.

Batun tsaro a filin jirgin sama na Nairobi
Daga BBC Reality Check

Asalin hoton, Public domain
Lamarin gano wannan mutum da ya makale a jikin jirgi daga filin jirgin sama na Jomo a Nairobi ya disa ayar tambaya da dama kan yadda lamarin tsaro yake a wajen.
Filin jirgin ya kasance karkashin tsatsanin tsaro saboda barazanar kungiyar al-Shabab da ke da sansani a makwabciyar kasar Somalia.
Wani lamarin irin wannan ya faru a shekarar 1997 lokacin da aka gano wani matashi a makale jikintayar gaba ta jirgin British Airways da ya taso daga Nairobi inda zai sauka a filin jirgin sama Gatwick.
Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Kenya ta ce an shirya wata tawaga domin bincikar yadda mutumin ya samu makalewa a jikin jirgin
Hukumar ta KAA tana gudanar da atisayen jami'an tsaro a filin jirgi - na baya-bayan nan shi ne wanda aka yi a watan Nuwambar 2018.

Ba wannan ce mutuwa ta farko da aka taba irin ta ba a hanyar filin jirgin sama na Heathrow.
A watan Yunin 2015 an gani gawar wani mutum a kan rufin hedikwatar notonthehighstreet.com a Richmond, a yammacin Landan, yayin da aka ga daya mutumin kuma cikin halin mutu kwakwai rai kwakwai bayan da dukkansu suka makale a jikin jirgin British Airways daya taso daga birnin Johannesburg na Afirka Ta Kudu.
A watan Agustan 2012 ma an samu gawar wani a karkashin wani jirgi a Heathrow bayan da jirgin ya isa Landan daga birnin Cape Town.













