An ceto Magajin Garin Daura daga masu satar mutane

Buhari

Asalin hoton, Presidency

Lokacin karatu: Minti 2

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta tabbatar da cewa ta kubutar da Magajin Garin Daura, kuma surukin dogarin Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.

Masu satar mutanen sun sace Alhaji Musa Umar ne a garin Daura a farkon watan Mayun 2019.

Mai bai wa shugaban kasa shawara kan kafofin sadarwa na zamani Bashir Ahmad ya wallafa sanarwar hakan a shafinsa na Twitter.

Kauce wa X
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X

Sai dai zuwa yanzu babu karin bayani kan yadda aka ceto Alhaji Musa Umar, amma Bashir Ahmad ya ce jami'an tsaron jihar Kano ne suka ceto shi.

Wannan layi ne

A ranar Laraba 1 ga watan Mayu ne 'yan bindiga suka kai hari garin Daura a jihar Katsina - wato mahaifar Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.

A wancan lokacin shugaban karamar hukumar Daura na riko Injiniya Abba Mato ya shaida wa BBC cewa bayan sallar magriba ne maharan suka kai wa garin farmaki.

Ya kuma ce sun sace surukin dogarin Shugaba Buhari, wato Magajin Garin Daura, Alhaji Musa Umar.

"Bayan shi da suka tafi da shi, maharan wadanda suka zo a mota daya, ba su harbi ko taba kowa ba," in ji Abba Mato.

Tun daga nan lokacin, ya ce jami'an tsaro suka dukufa aikinsu don ganin an kubutar da shi daga hannun maharan.

Kwana daya bayan faruwar lamarin ne kuma rundunar 'yan sandan Najeriya a jihar Katsina ta yi alkawarin ba da ladan naira miliyan biyar ga duk mai masaniya ko kuma karin bayani kan garkuwa da Alhaji Musa Umar, wanda hakimi ne a garin Daura.

Mai magana da yawun 'yan sandan jihar Gambo Isa, ya bayyana cewa wannan ladan za a bayar da shi ne domin taimaka wa 'yan sanda samun bayanai kan wadanda suka yi garkuwa da hakimin da kuma kokarin ganin cewa an ceto shi daga hannunsu.

Gambo ya shaida wa BBC cewa bayan sun samu labarin garkuwar da aka yi a Daura, sun yi sauri sun bi masu garkuwar inda har suka yi musayar wuta da su.