Zanga-zangar kyamar 'fyade' da ake zargin Fasto da yi

Masu zanga-zangar sun yi dandazo ne a yankin Guzape da ke Abuja, babban birnin Najeriya da wasu sassan birnin Legas da manufar bayyana wa mutane irin barnar da wasu fasto-fasto ke yi a majami'u.
Gomman masu zanga-zangar sun ta rera wake-waken yin Alla-wadai da kuma daga kwalaye masu rubutun da ke jan hankalin jama'a da ka da su saki jiki da fasto-fasto dinsu.
An dai gudanar da zanga-zangar ne da manufar nema wa wata wadda ta yi zargin faston cocin Commonwealth of Zion Assembly COZA, Pastor Biodun Fatoyinbo da yi mata fyade.
Masu fafutukar na kara kira ga mata da su fallasa masu irin wannan ta'ada kasancewar zamanin danne hakkin mata ya shude.




To sai dai yayin da masu zanga-zangar suke kokarin goyon bayan Bisola Dakolo, a gefe guda an samu wasu masu zanga-zangar da ke goyon bayan Pastor Biodun Fatoyinbo.

Me Bisola take zargin Fasto da shi?

Bisola Dakolo dai ta fito a wani bidiyo inda ta yi hira da wani dan jarida take sheda masa cewa Fasto Biodun ya yi mata fyade lokacin tana 'yar shekara 16.
Ta kara da cewa ya yi mata fyaden ne fiye da sau daya, inda a karon farko faston ya yi lalata da ita a cikin gidansu da misalin karfe shida na safe.
Da aka tambaye ta dalilin da ya sa ba ta yi ihu ba domin jama'a su kai mata dauki sai ta ce "Ya rufe min baki."
Bisola dai yanzu haka mai dakin fitaccen mawakin nan ce, Timi Dakolo kuma tana da yara.
Mene ne martanin fasto?

Kwatsam bayan kammala ibadar ranar Lahadi, sai Pastor Biodun ya fito ya yi wa mahalarta cocin nasa jan kunne cewa ka da su shiga rikici saboda zargin lalata mata.
Ya kara da yin kira ga magoya baya da su zama masu zaman lafiya ka da su tayar da zaune tsaye.
Sai dai a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma'a, Pastor Biodun Fatoyinbo ya ce sam bai taba yi wa wata mace fyade ba, inda ya yi barazanar kai Bisola gaban kuliya.
Ya kuma danganta ikrarin da wani yunkurin bata sunansa da na cocin.












