Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Dalilai bakwai da suke sa matasa kashe kansu
A baya-bayan nan ana yawan samun karuwar matasan da ke kashe kansu, al'amarin da masana ke cewa ya kamata a yi wa tufkar hanci tun kafin lamarin ya ta'azzara.
A makon da ya gabata ne dai kafafen watsa labarai a Najeriya suka yi ta wallafa wani labari na wani matashi dalibi a jami'ar Niger Delta, da ke Ammasoma na Kudancin karamar hukumar Ijaw da ke jihar Bayelsa.
An dai ce dalibin dan aji uku a tsangayar koyan aikin likita na jami'ar ya kashe kan nasa ne ta hanyar fadawa cikin ruwa sakamakon rashin cin jarrabawar da ya yi, al'amarin da ya sa tsangayar ta sa sunansa a jerin sunayen mutum 22 da jami'ar za ta kora.
Wata hanyar da matasan ke amfani da ita wajen kashe kan nasu ita ce amfani da maganin kwari da ake kira 'Sniper'.
Ko a makon da ya gabata sai da gwamnatin Najeriya ta sanar da haramta yin maganin kwarin a kasar da manufar dakile yawaitar kashe kan.
Hukumar Kula da Ingancin Abinci ta Najeriya, NAFDAC, ta ce tana son ganin an sauya kwalbar maganin kwarin ko hakan zai hana matasa shan sa.
Me ke sa matasa kashe kan nasu?
Masu nazarin zamantakewar dan adam irin su Farfesa Sadiq Radda na Jami'ar Bayero ta Kano ya zayyana dalilai guda bakwai da ya ce su ne suke jefa matasa halin kashe kai:
- Kuncin Rayuwa
- Takurawar iyaye
- Takurawar abokai
- Takurarwar makwabta
- Fina-finai
- Kafofin sa da zumunta na zamani
- Rashin hakurin matasa kan rayuwa
Ya ya za a magance matsalar?
Farfesa Sadiq Radda ya ce "magance batun kashe kai da matasa ke yi ba abu ne na mutum daya ba."
Ya kuma kawo wasu hanyoyi guda uku da ya ce idan aka bi su za a iya samun sauki:
- Ilimi: Ya kamata a bai wa matasa ilimin addini da na zamani domin sanin amfanin rayuwa.
- Wa'azi: Akwai bukatar malaman addini su mayar da hankali wajen yi wa matasa wa'azi kan illar kashe kai a addinance.
- Sa ido kan fina-finai: An bukaci iyaye da gwamnatoci su rinka tantance da sa ido kan irin fina-finan da matasa ke kallo.
Ko a farkon watan nan ma wata matashiya ta kashe kanta a jihar Kano da ke arewacin Najeriya wacce ake zargin takaicin sakin mahaifiyarta da mahaifinta ya yi ne ya sa ta aikata hakan.
Ga wata hira da BBC Hausa ta yi a watan Mayu da wasu likitocin kwakwalwa biyu kan irin wadannan lamurra shafinmu na Facebook .