Shugaban China yana ziyara a Koriya ta Arewa

Kim Jong-un na Koriya ta Arewa da Xi Jinping na China

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Sun sha haduwa a baya amma ba su taba kasancewa a Koriya ta Arewa tare ba

Kafar watsa labarai ta gwamnatin China ta ruwaito cewa Shugaba Xi yana ziyarar Koriya ta Arewar ne, bisa gayyatar takwaransa Kim Jong-un.

Mista Xi ya kasance Shugaban China na farko cikin shekara 14 da ke ziyara a kasar ta Koriya ta Arewa.

Kafin wannan ziyara, sau hudu shugaban na China yana karbar bakuncin takwaran nasa na Koriya ta Arewa.

Dukkanin shugabannin biyu a yanzu suna dambarwa da Amurka, inda China ke takaddama da ita a kan harkokin kasuwanci, ita kuma Koriya ta Arewar, suke wa juna kallon hadarin kaji da Washington din a kan shirinta na makaman nukiliya.

Gwajin makamai masu linzami na Koriya ta Arewa

Asalin hoton, AFP/KCNA VIA KNS

Bayanan hoto, China na son Koriya ta Arewa ta daina gwajin makamai masu linzami

Gwamnatin China ta kafe cewa ta amince da matsayar Koriya ta Arewa ta lalata makamanta na kare-dangi daki-daki, amma ita kuwa Amurka ta ce lalle ita so take ta ga Koriyar ta lalata wani babban bangare na makaman nata, kafin ta amince ta cire wa Pyongyang takunkumin tattalin arzikin da ta sanya mata.

China ita ce, kadai wata babbar kawa ga Koriya ta Arewa, a don haka Mista Kim zai iya amfani da wannan dama ya nuna wa gwamnatin Trump cewa yana da gaggan abokai masu karfin gaske a tare da shi.

Kim Jong-un and Donald Trump

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A watan Yuni na 2018, Kim Jong-un da Donald Trump sun hadu a karon farko

Ana ganin shugabannin biyu za kuma su tattauna tasirin takunkumin tattalin arzikin wanda China ta bayar da shawarar Amurka ta sassauta wa Pyongyang.

Yayin da rikicin China da Amurka kan kasuwanci ke ci gaba, Shugaban na Sin ya san cewa da wannan ziyara tasa Amurka za ta san cewa yana da tasirin fadi-a-ji ga Koriya ta Arewa a kan shirinta na nukiliya.