'Akwai hannun Yarima Ibn Salman a kisan Jamal Khashoggi'

Ibn Salman a wani taron kungiyar kasashen musulmi da aka gudanar a kasar Saudiyya

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Yarima Mohammed ya sha musanta cewa yana da masaniya kan kisan

An samu kwararan shaidu da ke nuna cewa Yarima Mai Jiran Gado na kasar Saudiyya, Mohammed Bin Salman da wasu manyan jami'an gwamnatin kasar na da hannu a kisan Jamal Kashoggi.

Wani rahoton wata mai bincike ta majalisar ta dinkin duniya, Agnes Callamard, ya ce shaidun da aka samu na nuna bukatar gudanar da bincike na gaskiya.

Wasu jami'an kasar Saudiyya ne dai suka kashe Kashoggi a ofishin jakadancin Saudiyyar da ke birnin Istanbul na kasar Turkiyya.

Hukumomin Saudiyyar sun kafe cewa ba Yarima Bin Salman ne ya ba su umarni ba.

Sannan suka yi watsi da rahotan na Majalisar ta Dinkin Duniya, suna masu cewa yana kunshe da kura-kurai.

Tuni dai Saudiyya ta fara yi wa mutum 11 shari'a a asirce kan kisan Khashoggi, inda hukumomin ke son yanke wa mutum biyar daga ciki hukuncin kisa.

To sai dai Misis Callamard ta ce shari'ar ta saba da ka'idodjin kasa da kasa, inda ta nemi da a dakatar da ita.

Kafin kisan Kashoggi, Saudiyya ta haramta masa shiga kasar
Bayanan hoto, Kashoggi yana yi wa Saudiyya kakkausan suka

Me ya faru?

A ranar 2 ga watan Octoba na 2018, Jamal Khashoggi ya shiga ofishin jakadancin saudiyya da ke Istanbul, inda matar da zai aura, Hatice Cengiz ta jira shi a wajen ofishin amma ba ta Khashoggi ya fito ba.

A ranar 4 ga watan na Octoban 2018 din ne dai kasar Saudiyya, a karon farko ta sanar da cewa Kashoggi ya yi batan dabo, bayan fitowarsa daga ofishin jakadancin.