Trump ya kaddamar da neman sake takara a zaben 2020

Donald Trump

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Shugaban Amurka Donald Trump na fatan samun wa'adi na biyu a zaben 2020

Shugaban Amurka Donald Trump a hukumance ya kaddamar yakin neman sake takararsa, inda ya bukaci magoya bayansa su "tabbatar da wannan tafiya" tsawon wata shekara hudu mai zuwa.

Shugaban dan jam'iyyar Republican ya bayyana aniyarsa ce a gaban dubban magoya baya yayin wani gangami a cikin Florida, inda ya bayyana jihar da cewa "gidana na biyu".

Mista Trump ya kuma yi amfani da sanarwar wajen yin dirar mikiya a kan 'yan Dimokrat, inda ya zarge su da kokarin "tarwatsa kasar".

Binciken ra'ayoyin jama'a na farko-farko na nuna Mista Trump a bayan wasu 'yan jam'iyyar Dimokrat da ke da yiwuwar kalubalantar takararsa.

"Za mu sake tabbatar da ganin Amurka ta zama kasaitacciyar kasa," shugaban ya bayyana a taron na Orlando da maryacen Talata. "A daren nan ga ni na tsaya gabanku don a hukumance na kaddamar da yakin neman wa'adi na biyu a matsayin shugaban Amurka."

"Gaba daya mun tunkari wata tafiyar siyasa rusasshiya kuma mun dawo da gwamnati ta jama'a kuma don jama'a," ya tunasar game da yakin neman zabensa na farko, inda ya ayyana lamarin da cewa "wata gagarumar tafiyar siyasa ce".

"Matukar kuka tabbatar da wannan tafiya, dumbin abubuwan alheri na nan tafe. Muna hango alheri a gabanmu."

Shugaba Trump ya koma kan alkawarin yakin neman zabensa na 2016 game da murkushe haramtattun bakin haure, ya kuma yi gargadin cewa masu kalubalantarsa na jam'iyyar Dimokrat na son halasta wa 'yan ci-rani tsallako iyakar kudancin kasar.

Kwana guda kafin nan, shugaban ya wallafa sakon Tiwita cewa hukumomi za su fara "fitar da miliyoyin bakin haure wadanda suka shiga Amurka ta haramtacciyar hanya".

Da wa Trump zai yi takara a 2020?

Facewall promo