Mohammed Morsi: Tsohon shugaban Masar ya mutu a kotu

Tsohon shugaban Masar, Mohammed Morsi, ya rasu bayan da ya yanke jiki ya fadi a lokacin da ake ci gaba da yi masa shai'a a gaban wata kotu, a cewar hukumomin kasar.

Kafar yada labaran talabijin ta kasar Masar ta ce tsohon shugaban kasar ya mutu ne yayin da ake zaman kotu don sauraron kararsa da ake yi.

Rahotanni sun ce ya suma ne a yayin zaman kotun inda ake tuhumarsa da laifukan cin amanar kasa, jim kadan bayan sumar tasa sai ya cika.

Ya mutu yana da shekara 67.

A shekarar 2013 ne sojoji suka hambarar da gwamnatinsa.

Wane ne Morsi?

An haifi Morsi ne a kauyen El-Adwah a gabar kogin Nilu a lardin Sharqiya a 1951.

Ya yi karatu a fannin injiniya a Jami'ar birnin Alkahira a shekarun 1970 kafin ya tafi kasar Amurka inda ya kammala digiri na uku a can.

Kungiyar 'yan uwa Musulmi ta Brotherhood ta tsayar da shi dan takarar shugabancin kasar Masar a shekarar 2012.

Bayan da ya samu nasara a zabe, ya yi alkawarin cewa "gwamnatinsa za ta tafi da duka 'yan Masar".

Sai dai masu suka sun ce gwamnatinsa ta kasa cirewa 'yan kasar kitse a wuta.

An zarge shi da barin masu tsananin kishin addinin Islama cin karensu ba babbaka a fagen siyasar kasar da rashin iya tafiyar da tattalin arzikin kasar, batun da shi da magoya bayansa suka musanta.

Daga nan ne aka fara samun dimbin masu zanga-zanga adawa da gwamnatin Morsi a titunan kasar lokacin bikin cika shekara daya da hawansa mulki a ranar 30 ga watan Yunin shekarar 2013.

'Yan kwanaki bayan fara zanga-zangar a ranar 3 ga watan Yuli sojoji suka dakatar da kundin tsarin mulkin kasar, inda suka sanar da kafa wata gwamnatin rikon kwarya kafin gudanar da sabon zabe.

Bayan haka sai sojojin suka kama Morsi, wanda ya yi watsi da matakin hambarar da gwamnatinsa.