An bai wa Aminu Ado Bayero sarautar Bichi

Aminu Ado

Asalin hoton, Facebook Kano

Gwamnatin jihar Kano ta tabbatar cewa Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya bai wa Aminu Ado Bayero sarautar daya daga cikin sababbin masarautun da aka kirkiro a Kano.

A ranar Juma'a ne aka bai wa dan marigayi Sarki Ado Bayero wannan sarauta ta sabuwar masarautar Bichi.

Wani makusancin sabon sarkin Bichi da ya bukaci a sakaya sunansa, ya tabbatar wa BBC wannan al'amari, ya kuma ce tuni Aminu Bayero ya karbi sarautar.

Mai martaba sabon sarkin Bichi shi ne Wamban Kano na yanzu, kuma yana daya daga cikin manyan 'ya'yan marigayi Ado Bayero.

Gwamnatin jihar Kano ta sanya ranar Asabar don bai wa sabbin sarakunan sandunan girma.

Sauran sarakunan sabbin masarutun, kafin wannan nadi, hakimai ne a garuruwansu a masarautar Kano.

Kuma sun hada da Sarkin Karaye Alhaji Dr Ibrahim Abubakar da Sarkin Bichi Alhaji Aminu Ado Bayero da Sarkin Rano Alhaji Tafida Abubakar Ila da kuma Sarkin Gaya Alhaji Ibrahim Abubakar Gaya.

Wasu bayanai dai sun nuna cewa tuni 'yan gidan sarautar Kano suka yi ta kamun kafa a wajen gwamna don ganin an nada su sarautar.

Rarraba masarautun Kano

A ranar Laraba ne Gwamna Ganduje ya sanya hannu kan dokar da majalisar dokokin jihar ta amince da ita a ranar Litinin, ta neman kara yawan marautun jihar.

Lamarin dai ya janyo ce-ce ku-ce a tsakanin al'ummar kasar baki daya ba ma na Kano kawai ba.

Karya karfin Sarki Sunusi? Sharhi, Halima Umar Saleh

Sarkin Kano

Asalin hoton, Kano Emirate

Wannan dai wani yunkuri ne da ake alakantawa da kokarin rage karfi ko karya lagon masarautar Kano.

Haka zalika, akwai wadanda suke ganin hakan ba ya rasa nasaba da rashin jituwa da ake gani akwai tsakanin Gwamna Ganduje da Sarki Sanusi na Biyu.

Wasu rahotanni sun ta bayyana cewa Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ne ya aike wa majalisar jihar kudirin bukatar amincewa da sake kirkirar wasu sabbin masarautu a jihar.

Wasu majiyoyin cikin gida kuma na cewa matakin ba ya rasa nasaba da mara baya ga wani bangare da ake zargin sarkin na yi a fanin siyasar jihar.

Sai dai Shugaban masu rinjaye na Majalisar Kanon Baffa Baba Dan'agundi, ya ce babu hannun bangaren zartarwa cikin wannan al'amari, bukata ce kawai ta al'ummar yankunan da aka nada.

Waiwaye

Kusan shekara 40 a baya, an taba kirkirar sabbin masarautu zamanin tsohon Gwamnan Kano Abubakar Rimi, lokacin da aka samu sabani tsakaninsa da marigayi Sarki Ado Bayero.

Sai dai daga baya a 1983 Gwamnatin Sabo Bakin zuwo ta rusa wadannan masarautu, inda aka sake mayar da su karkashin masarauta guda.

An jima dai ana yada jita-jitar takun-saka tsakanin Gwamnan mai ci da kuma Sarki Sunusi na Biyu, abin da ya kai ga a watanni baya aka ce zai tube sarkin.

Ado bayero

Asalin hoton, Kano Emirate

Bayanan hoto, Abubakar Rimi ya taba kirkirar sabbin masarautu lokacin da suka samu sabani tsakaninsa da Sarki Ado Bayero

Yadda tsarin masarautun zai kasance

Sarkin birni da kewaye na da kananan hukumomi 10 a karkashinsa da suka hada da:

  • Fagge
  • Nassarawa
  • Gwale
  • Dala
  • Tarauni
  • Kano Municipal
  • Minjibir
  • Ungogo
  • Kumbotso
  • Dawakin Kudu

Sarkin Rano kuma zai kasance yana da kananan hukumomi kamar haka:

  • Rano
  • Bunkure
  • Takai
  • Kibiya
  • Sumaila
  • Doguwa
  • Kiru
  • Bebeji
  • Kura

Sarkin Gaya kuma zai kasance yana da kananan hukumomi kamar haka:

  • Gaya
  • Ajingi
  • Albasu
  • Wudil
  • Garko
  • Warawa
  • Gezawa
  • Gabasawa

Sarkin Bichi kuma zai kasance yana da kananan hukumomi kamar haka:

  • Bichi
  • Bagwai
  • Shanono
  • Tsanyawa
  • Kunci
  • Makoda
  • Danbatta
  • Dawakin Tofa
  • Tofa

Sarkin Karaye kuma zai kasance yana da kananan hukumomi kamar haka:

  • Karaye
  • Rogo
  • Gwarzo
  • Madobi
  • Rimin Gado
  • Garun Malam

Wata sanarwa da gwamnatin jihar Kano ta fitar ta ce Sarkin Birnin Kano da Kewaye Muhammadu Sanusi II shi ne zai samu Shugaban majalisar zartarwa na Masarautun guda biyar, sannan kuma Sarkin Rano shi zai zama mataimakinsa.

Sannan shugabancin wannan majalisa zai zama na karba-karba ne inda kowane shugaba zai shekara biyu, amma bayan kammala wa'adinsa, gwamnatin jiha na da hurumin kara masa wani wa'adin karo na biyu.Sannan sauran 'yan majalisar masarautun sun hada da:

  • Sakataren gwamnatin jiha
  • Kwamishinan kananan hukumomi
  • Shugabannin kananan hukumomi
  • Hakimai masu nada sarki bibbiyu daga kowace masarauta
  • Wakilcin mutum biyar da gwamna zai nada.

Sanarwar ta kuma ce: "Sako na karshe kuma shi ne sabuwar dokar ba ta hana wani wanda ya gaji sarautar Kano daga sauran sababbin masarautun guda hudu zama Sarkin Birnin Kano da Kewaye ba, in dai har sun gada."