Ina jin kunya na ga 'yan matan Najeriya na karuwanci - Limamin Abuja

Mata biyu a tsaye a bakin titi

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Ana fasa kawaurin daruruwan mata matasa daga Najeriya zuwa Turai don karuwanci

Babban limamin katolika na Abuja, Cardinal John Onaiyekan ya bukaci gwamnatin Najeriya ta kara himma wajen dakatar da fasa-kwaurin matasa da kuma kaurar da suke yi zuwa Turai ta hanyar inganta halin rayuwarsu a kasar.

Babban limamin na katolika Cardinal Onaiyekan ya ce "ina tafe a titunan birnin Rum da Milan da Naples sai in ga 'ya'yanmu mata a kan titi suna karairaya da nufin sayar da kansu. Ina jin kunya. Kuma ba za ma ka iya magana da su ba saboda daga kauye aka dakko su babu ilimi."

A cewarsa: "Abun kawai da suke koyo a kan titunan Italiya shi ne abin da suke bukata don sana'arsu. Abin kunya ne."

Duk shekara, ana fasa kwaurin dubban 'yan mata daga Nijeriya, inda kuma wasunsu ke fada wa tarkon mayaudara wadanda ke jefa su cikin harkar karuwanci.

John Onaiyekan ya ce ana iya kauce wa fada wa irin wannan hali, don haka ya yi kira ga gwamnatin Nijeriya ta dauki mataki.

Acibishof Onaiyekan ya kuma soki lamirin jami'an gwamnati saboda mayar da hankali wajen gina kawunansu ta hanyar gina maka-makan gidaje da fantsama yawace-yawace a kasashen duniya.

Hukumar kula da kaura ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce ana fasa-kwaurin dubban 'yan mata duk shekara inda ake fitar da su bayan an yi romon bakan cewa za a sama musu ayyukan yi, amma daga bisani da yawansu sai a tursasa musu shiga karuwanci.

Babban limamin ya ce kamata ya yi gwamnati ta gyara Nijeriya ta yadda masu yawon bude idanu za su rika tururuwa shigowa, maimakon a rika kwadaitawa matasanta ayyukan yi ana fataucinsu saboda rashin damammaki.