Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Zamfara: Shin kashe-kashen gilla karuwa suke a Najeriya?
- Marubuci, Daga Sashen bin diddigi na BBC News
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
Ana ci gaba da damuwa a Arewacin Najeriya kan yawan hare-hare da kuma satar mutane da ake yi a jahar Zamfara.
A cikin wani bidiyon da aka wallafa a baya-bayan nan, wata 'yar jarida a kasar Kadaria Ahmed ta soki gwamnati kan ikrarinta na cewa ana ta samun karuwar kashe-kashe a yankin.
''A kullum dai muna binne a kalla mutum 30 ko 40 ko kuma 50,'' kamar yadda ta fadi hakan a wani bidiyo, da kuma a wani jawabin da ta gabatar a talbijan wanda aka kuma yada sosai a shafukan sada zumunta.
Ta ce ana kashe mutane a Zamfara fiye da yadda ake kashe mutane a Borno da Adamawa da kuma Yobe, jihohi kenan a yankin arewa maso gabashin Najeriya wadanda 'yan kungiyar Boko Haram su ke yawan kai hare-hare.
To me ke faruwa a Zamfara, kuma yawan tashin hankali na karuwa ne a jihar?
Zamfara dama ta dade tana fama da matsalar sace-sacen dabobi, da dauke mutane domin samun kudin fansa da kuma kai hare-hare kan al'ummomi, wanda hakan ya tilasta wa wasu mazauna yankin suka hada kai wajen samar da kungigoyin 'yan banga.
A 'yan kwannakin nan dai, an samu karuwar hakar ma'adinai ba ta halattacciyar hanya ba a yankin mai dumbin arzikin ma'adinai, hakan ya janyo shigowar baki da dama, daya daga cikin abubuwan da ke kara hana zaman lafiya a yankin kenan.
A farkon watan Afrilun 2019, gwamnati ta mayar da martani kan damuwar karin hare-haren da a ke kaiwa, ta kuma dakatar da dukkanin ayyukan hakar ma'adinai a jahar, tare da aika dakarun tsaro zuwa yankin.
Wata cibiyar kula da yawan tashe-tashen hankula a Najeriya - The Nigeria Security Tracker, wanda hukumar kula da harkokin kasashen waje a birnin Washington (CFR) ta kafa, tana kula da yawan tashe-tashen hankula ta hanyar bincike kan rahotannin da kafafen yada labarai a kasar ke wallafawa.
Wannan na nuna cewa an samun karuwar kashe-kashe a cikin 'yan makkonin da suka gabata.
A cewar wadanan nambobin, tun farkon 2019, an samu mutuwar fararen hula 262. A cikin 2018 gaba daya an samu 288, a 2017 kuma 52.
Hasashen na CFR ya nuna karuwar kashe 'yan kungiyar bindiga - a ciki har da 'yan ta'adda da 'yan banga da kuma duk wanda ya ke da hannu a harkokin rashin gaskiya.
Amma, yawan mutanen da ke mutuwa a kowace rana bai kai 30 da 50 inda Kadaria Ahmed ta bayyana cewa ana samu ba.
Fararen hula 262 ne suka mutu a cikin kwana 100 na wannan shekarar, hakan na nufin kenan mutum biyu ko uku ne ke rasa rayyukansu a kowace rana, duk da yawan da CFR ta fitar ba ta bayyana cewa yawan wadanda ke rasa rayukansu na karuwa ba.
Kwatanta Zamfara da sauran jihohin Arewacin Najeriya
A cikin bidiyonta, Kadaria Ahmed ta kuma yi zargin cewa an fi samun tashe-tashen hankula a Zamfara fiye da yadda ake samu a jihohin da ke yankin arewa maso gabashin kasar, inda 'yan Boko Haram su ke yawan kai hare-hare.
Idan aka dauki dukkanin mace-macen fararen hula da aka samu tun farkon watan Maris har zuwa shida ga watan Afrilu, an samu mutuwar mutum 169 a Zamfara a cewar CFR - an kwatanta wannan da mutum 28 da suka mutu a Borno da kuma 14 a Adamawa.
Ba a samu irin lamarin a Yobe ba.
Saboda haka hasashen Kadaria Ahmed daidai yake, inda ta ce an fi samun mace-macen mutane a Zamfara idan aka kwatanta su da wadancan sauran jihohin.
Raguwar yawan kashe-kashen da ake yi a Borno da Adamawa da kuma Yobe na faruwa ne sakamakon yawan kwace yankunan da ke karkashin ikon 'yan Boko Haram da ake yi tun a shekara ta 2015.
Karin bayani game da Zamfara:
- Kashi 67.5 na mutanen jihar na cikin talauci (kashi 62 kenan cikin 100 na masu fama da talauci a kasar)
- Yawan mutanen da ke fama da rashin ilimi: kashi 54.7 cikin 100
- Taken jihar: Noma shi ne abin da muke alfahari da shi
- Mazauna jihar yawanci manoma ne daga al'ummomin Hausawa da kuma Fulani
- Yawan al'umma : Miliyan 4.5 ( hasashen da aka yi a 2016)
- Ma fi yawan al'ummar jihar Musulmai ne
- Ita ce jiha ta farko da ta kaddamar da shari'ar Musuluncia shekarar 2000