Mafi karancin albashi: Majalisa ta amince da naira dubu 30

Labour union

Asalin hoton, Stringer

Majalisar dattawan Najeriya ta amince da kudirin dokar kara mafi karancin albashi zuwa naira 30,000.

Majalisar dattawan ta amince da dokar ne ranar Talata bayan da kwamitin da ta kafa kan mafi karancin albashin ya mika mata rahoton da ya hada.

A shekarar 2018, majalisar wakilan Najeriya ta sa hannu kan kudirin dokar da ya tanadi a biya naira 30,000 a matsayin mafi karancin albashi ga ma'aikatan gwamnati na jiha da na tarayya.

Shugaba Muhammadu Buhari dai ya aika kudirin zuwa ga Majalisar Kasa don neman amincewarta.

Sanata Francis Alimikhena ya mika rahoton kwamitin ne ga 'yan majalisar inda daga nan ne 'yan majalisar suka rarraba kansu zuwa kwamiti-kwamiti kuma suka fara duba abubuwan da dokar ta kunsa bi da bi.

Sanata Ahmed Lawan, shugaban masu rinjaye na jam'iyyar APC mai mulki ya ce kwamitin ya cika alkawarinsa na yankarwa 'yan Najeriya "mafi karancin albashi mai tsoka."

Ya kuma ce dole ne sauran 'yan majalisa su yaba wa aikin da kwamitin ya yi, sannan ya ce gwamnati ta daina jira sai ma'aikata sun yi barazanar zuwa yajin aiki kafin ta dauki mataki.

Bayan da majalisar ta amince da dokar ne Shugaban Majalisar Bukola Saraki ya jinjina wa shugabannin kungiyar kwadago, inda ya ce bai dace gwamnati ta rika jira sai an yi yajin aiki ba kafin ta ba ma'aikata abin da suke bukata.

A watan Janairun da ya gabata ne Majalisar Wakilai ta amince da mafi karancin albashin duk da cewa Majalisar Kasa ta yanke mafi karancin albashin a naira 27,000.