Talauci ya sa matar aure zaman gidan yari da jaririyarta

Woman

Asalin hoton, Getty Images

Mai dakin gwamnan jihar Kebbi, Dakta Zainab Atiku Bagudu ta biya wa wata mata da ke tsare a gidan yari tarar naira 15,000.

Dakta Zainab ta ce akwai shirinta na biya wa fursunoni tara tare wanda take yi tare da hadin gwiwar Kungiyar Mata Lauyoyi ta Najeriya da wasu kungiyoyin.

Ta ce su kan ziyarci gidajen yari don biyan tarar kuma a irin wannan ziyarar ne a daya daga cikin gidajen yarin da ke jihar Kebbi ta ga wannan mata.

Ta ce ta ga mata uku a daure kuma wannan matar ta fi daukar hankalinta saboda tana rike da 'yar jaririyarta.

Mai dakin gwamnan ta bincika sai aka bayyana mata cewa an yanke wa matar daurin wata shida ne ko kuma biyan naira 15,000 saboda fada da ta yi da makwabciyarta.

Dakta Zainab ta biya kudin tarar tare da sa mutanen da ke yi mata aiki su yi wa matar rakiya har gida.

Matar dai ta fi wata daya a daure kafin biyan tarar.

Dakta Zainab ta ce talauci na daya daga cikin abubuwan da ke haddasa tashin hankali a wasu yankunan karkara a Najeriya.

"Da wanne za su ji? Kila babu abinci, ga rigimar yara. Shi ya sa dole mu rika sassauta wa juna. Ba ko wane laifi ne ya kamata a kai mutum gidan yari ba, ko mace ko namiji", a cewarta.

Ta kuma yi kira ga 'yan majalisar Najeriya da su duba dokokin kasar kan yawan kai mutane gidan kaso.

"A kasashen waje, misali wannan matar sai a sa ta tayi shara ko wani abu makamancin haka, amma ba dauri ba."

Cikin matan da matar gwamnan ta gani a tsare dai har da wadda ta yi kisan kai.