Mota ta kashe mutane 12 a kasuwa a Kebbi

Kebbi State

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Motar ta kufcewa direban ne inda ya fada wata kasuwa da ke bakin titi.

Wata babbar mota ta kashe wasu masu saye da sayarwa 12 a gefen titi ranar Litinin a karamar hukumar Jega da ke jihar Kebbi.

Rahotanni sun bayyana cewa motar ta kufcewa direban ne inda ya fada wata kasuwa da ke bakin titi.

Wani ganau ya ce hakan ya faru ne yayin da direban ya yi kokarin gujewa yin taho mu gama da wata karamar motar, wacce ta taho daga titin da ya fito daga garin Yauri.

Wani wanda ya shaida afkuwar hatsarin Adamu Jega, ya ce da mutanen ba su ankara da kufcewar motar ba, da adadin mutanen da suka rasa rayukansu ya fi haka.

Wadanda suka rasa rayukan nasu dai a cewar wata majiya sun hada da mutane bakwai masu sana'a a gefen titi da kuma wasu mutane biyar da ke cikin motar.

Haka ma wasu mutane kusan ashirin sun samu raunuka in ji Akilu Musa Jega wani jami'i a kungiyar direbobi ta kasa reshen garin na Jega.

Salwantar rayuka sakamakon hadarin manyan motoci ko jiragen ruwa wani abu ne da ke son zama jiki a jihar ta Kebbi musamman a kan wannan hanyar.

Wannan ba ya rasa nasaba da cewa ita ce ke sada jihar da babbar cibiyar kasuwancin kasar wato Legas.

A watan jiya, wasu fataken shanu 15 sun rasa rayukkansu a jihar lokacin da babbar motar da suke tafiya a ciki ta kauce hanya ta kuma kife.