Christchurch: An kashe mutum 49 a masallaci a New Zealand

Armed police patrol following a shooting resulting in multiply fatalies and injuries at the Masjid Al Noor on Deans Avenue in Christchurch, New Zealand, 15 March 2019.

Asalin hoton, EPA

Kimanin mutum 50 ne aka kashe, 20 kuma suka ji rauni bayan wani hari da aka kai wasu masallatai biyu a birnin Christchurch da ke kasar New Zealand.

Firai ministan Australia Scott Morrison ya bayyana maharin, wanda yake da takardun na Australia, da " wani dan ta'adda."

'Yan sanda sun ce sun kama mutumin da ake zargi da kai hari kuma za su gurfanar da shi a gaban kotu ranar Asabar da safe.

Hakazalika ana tsare da wasu mutum biyu, kuma an kama wasu makamai, a cewar Kwamishinan 'Yan sanda Mike Bush.

Sai dai 'yan sandan sun ce daya daga cikin mutanen da suke da hannun, sun fahimci cewa ba shi da hannu a harin, kuma jami'ansu suna ci gaba da binciken sauran mutum biyun.

Wannan harin shi ne mafi muni da aka taba kai wa kasar New Zealand.

Abin da aka sani kawo yanzu?

An fara kai wa masallacin Al Noor mosque hari ne wanda yake tsakiyar birnin Christchurch. Wasu da suka shaida al'amarin sun ce sun rika gudu don neman tsira da rayuwarsu, a daidai lokacin da suka ga wasu mutane suna fitowa daga cikin ginin jina-jina.

An sa mutanen da ke masallaci na biyu da ke wajen birnin Linwood ficewa daga cikinsa. Kuma 'yan sanda sun kwanshe wani abin fa da aka makala a jikin wata mota, in ji Mista Mike.

Mahukunta sun umarce a rufe duka masallatan da ke birnin har sai abin da hali ya yi.

A lokacin da yake magana da manema labarai, Mista Bush ya ce 'yan sanda suna aiki don ganin sun kama sauran mutanen da ake zargi da hannu a harin. .

Ya ce an gano wasu makamai da wurin da harbe-harben biyu suka faru.

New Zealand

An rika kai mutanen da suka jikkata asibitin birnin inda aka tsaurara matakan tsaro.