Bayanan hoto, Al'amarin ya faru ne unguwar a Itafaji da ke yankin Legas Island.
Bayanan hoto, Ginin dai mai hawa uku ne kuma akwai mutane da dama a cikinsa a lokacin da abin ya faru.
Bayanan hoto, Tuni jami'an agajin gaggawa da 'yan kwana-kwana da masu aikin ceto na sa kai suka yi ta kokarin ciro da wadanda abun ya rutsa da su a karkashin baraguzan ginin.
Bayanan hoto, Tuni dai aka garzaya da wasu daliban babban asibitin gwamnati da ke Marina, yayin da iyaye kuma ke turuwar zuwa wajen don duba 'ya'yansu.
Bayanan hoto, Wasu ganau mazauna yankin sun shaida wa BBC cewa sau biyu gwamnati ke bai wa masu ginin umarnin cewa ka da a kara dora wani bene a kai, "amma sai suka yi biris da wannan umarni," in ji wani mutum.
Bayanan hoto, Ana yawan samun rushewar gine-gine a Najeriya musamman a manyan biranen kasar kamar Legas da Fatakwal da Abuja.
Bayanan hoto, Wannan al'amari dai ya jefa mazauna yankin cikin matukar rudani da kaduwa.