INEC ta sa ranar sake zaben wasu mazabun Kano

Asalin hoton, Getty Images
Hukumar zaben Najeriya INEC ta fadi ranar da za ta gudanar da zabuka a jihohin da ta sanar da cewa ba a kammala zabensu ba.
Cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Talata, INEC ta ce a ranar 23 ga Maris ne za a gudanar da zaben a jihohin guda shida da ba a kammala zaben gwamnoni da na 'yan majalisa jiha ba.
Jihohin da za a sake zaben wasu mazabu sun hada da Kano da Bauchi da Sokoto da Filato da kuma Adamawa.
INEC ta ce za a yi zaben ne a wasu mazabun jihohin da ba a kammala ba, lamarin da ya hana a sanar da wanda ya lashe zaben na gwamna da aka gudanar a ranar 9 ga Maris.
Hukumar ta ce za ta sanar da mazabun da za a sake zabukan da kuma wadanda suka cancanci kada kuri'a a rumfunan zaben ya shafa.
Hukumar ta bayyana dalilan da suka sa ba a kammala zabukan ba a jihohin guda shida, wadanda suka hada da matsalar na'urar card reader da jefa kuri'a fiye da kima da kuma tarwatsa wasu rumfunan zabe.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Fafatawar a zabukan da za a sake ta shafi manyan jam'iyyu biyu na Najeriya APC da PDP da za a yi a zabukan gwamnoni da za a sake a jihohi guda shida.
Kusan dai jihohin da aka sanar da ba a kammala zabensu na gwamna ba, jihohi ne da babbar jam'iyyar hamayya PDP ke kan gaba.
Jihohi 22 ne Hukumar INEC ta kammala zabe tare da sanar da wanda ya lashe zaben na gwamnoni da 'yan majalisa.











