Yadda aka gudanar da zaben gwamnoni a Najeriya

Wannan shafi ne da ke kawo rahotanni da bayanai da kuma sharhi kan yadda aka gudanar da zaben gwamnoni da na 'yan majalisar jihohi a Najeriya.

Rahoto kai-tsaye

Mustapha Musa Kaita, Mohammed Abdu and Awwal Ahmad Janyau

  1. Bankwana

    Masu bibiyarmu a wannan shafi duka-duka a nan muka kawo karshen bayanai na kafin zabe da ranar zabe da kuma na bayan fadar sakamako da muka yi ta kawo muku.

    A madadin daukacin ma'aikatan BBC Hausa, musamman wakilanmu da suka yi ta aiko da rahotanni daga sassan Najeriya da editan BBC Hausa Jimeh Saleh da Yusuf Yakasai da Naziru Mika'il da suka yi ta sa ido kan yadda abubuwa ke gudana.

    Sai kuma wadanda suka yi ta kula da wannan shafi kamar Nasidi Adamu Yahaya da Muhammad Abdu Mamman Skipper da Umar Rayyan da Halima Umar Saleh da Mustapha Kaita da Awwal Janyau da Sani Aliyu da Abdulbaki Jari da Fatima Othman da Umar Mika'il da Sadiya Umar Tahir da Abdullahi Bello da Muhammad Auwal Mu'az da kuma Abubakar Abdullahi, muke muku fatan alkahiri.

    Ku biyo mu a ranar jajibirin zabe zagaye na biyu da INEC ta ce za a gudanar a wasu jihohi a Najeriyar domin kawo maku wasu bayanai da rahotanni kai tsaye.

    Allah ya ba mu alkhairi, Ameen summa ameen.

  2. Muna kawo muku labarai kai tsaye a BBC Hausa Facebook

  3. Shirin rana kai tsaye daga shafinmu na Facebook

  4. Darius Ishaku ya ci zaben Taraba

    Hukumar INEC ta bayyana Darius Ishaku na jam'iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben jihar Taraba da kuri'u 520,433 sai kuma abokin karawarsa na jam'iyyar APC Sani Danladi ya samu kuri'u 362,735.

    Twitter/@dariusdishaku

    Asalin hoton, Twitter/@dariusdishaku

  5. Ra'ayoyi daga shafin Twitter

    Kauce wa X, 1
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X, 1

    Kauce wa X, 2
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X, 2

    Kauce wa X, 3
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X, 3

  6. PDP ce ta lashe zaben jihar Imo

    Hukumar zaben Najeriya INEC a jihar Imo ta bayyana tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar Wakilan Najeriya, Emeka Ihedioha, a matsayin wanda ya lashe zaben jihar.

    Sai da ya samu kuri'u 273,404, kafin ya doke sauran abokan karawarsa 69 ciki har da wanda ya zo na biyu, Uche Nwosu, na jam'iyyar Action Alliance wanda ya samu kuri'u 190,364.

    bbc

    Asalin hoton, National Assembly

  7. Kun san Sanatocin da za a bai wa takardar shaidar lashe zabe?

    Hukumar zaben Najeriya INEC ta ce za ta ba sanatoci da 'yan majalisar wakilai takardar shaidar lashe zaben ranar 23 ga watan Fabrairun bana.

    Sai dai hukumar ta ce wadanda sunayensu suka bayyana a shafinta na Intanet ne kawai za ta bai wa takardar.

    Kawo yanzu sanatoci 100 ne cikin kujeru 109 da kasar take da su hukumar ta bayyana sunayensu.

    Zaben Nigeria

    Asalin hoton, Nihgerian Senate

  8. Za a bai wa Sanatoci da 'yan majalisar wakilai shaidar cin zabe

    Hukumar zabe ta kasa, INEC ta sanar cewar za ta bai wa Sanatoci da kuma 'yan majalisar wakilain Najeriya shaidar takardar cin zaben da aka gudanar ranar 23 ga watan Fabrairu a fadin kasar.

    Hukumar ta tsayar da ranar Alhamis domin bai wa wadan da suka yi nasara takardar shaidar a taron da za ta gudanar a International Conference Center da ke Abuja.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  9. Muna kawo muku labarai kai tsaye a BBC Hausa Facebook

  10. Barkanmu da kasance wa a shirinmu na kai tsaye

    Sunana Mohammed Abdu Mamman Skeeper zan dora kan sharin kai tsaye na zaben gwamnoni da na majalisar dokoki na jihohin Najeria da aka gudanar tun a ranar Asabar.

    Tuni dai a wasu jihohin an sanar da sakamakon zaben, yayin da a wasu kuma ba a kammala ba, a babban birnin tarayya kuwa zaben shugaban karamar hukuma aka yi da na kansilo.

    Da fatan za ku ci gaba da bibiyar shirin da muke kawo muku shi kai tsaye.

    Za ku iya bayar da gudunmawarku a BBC Hausa Facebook da Tuwita da Instagram a BBC Hausa.com.

    Mau'du'in mu shi ne #BBCNigeria2019, #NigeriaDecides2019

  11. Sai gobe, Sakamakon zaben gwamnoni

    A nan za mu dakatar da kawo bayanai da rahotanni da sharhi kai-tsaye da muke kawo wa kan sakamakon zaben gwamnoni a jihohin Najeriya.

    Da fatan za ku kasance da mu a ranar Laraba domin ci gaba da kawo bayanai kai-tsaye.

    Awwal Ahmad Janyau ne ke maku sallama.

  12. Yadda ake jiran sakamako a Taraba, Sakamakon zaben gwamnan Taraba

    Mutane na bacci a babbar cibiyar tattara sakamako a Jalingo yayin da suke jiran sakamakon Sardauna, karamar hukuma ta karshe da ta rage a bayyana sakamakon gwamna a jihar Taraba.

    Taraba
    Taraba
    Taraba
  13. 'Mun yi maraba da sakamakon zaben gwamnan jihar Kano', Zaben gwamnan Kano

    Bayanan sautiMuryar Kwamishinan yada labarai na jihar Kano Malam Muhammad Garba

    Gwamnatin jihar Kano ta yaba wa kokarin hukumar INEC game da yadda ta gudanar da zabe a jihar, kamar yadda Kwamishinan yada labarai na jihar Kano Malam Muhammad Garba ya shaida wa BBC.

    "Da farko ya kamata a fara ne da yaba wa hukumar zabe ta INEC, saboda jajircewar da suka nuna," in ji shi.

    Daga nan ya ce za su sake yin shiri don tunkarar zabukan a mazabu a kananan hukumomi 22.

    Har ila yau ya ba da tabbacin cewa ba su karaya ba.

    Babban jami'in tattara sakamako zabe a Kano Farfesa B.B Shehu ne ya sanar da cewa ba a kammala zabe a Kano ba.

    A cewarsa Abba Kabir Yusuf na babbar jam’iyyar hamayya PDP ya samu kuri’a 1,014,474 yayin da gwamna mai ci na Jam’iyyar APC Abdullahi Umar Ganduje ya samu kuri’a 987,819.

    Jam’iyyar PRP ce ta zo a matsayi na uku da kuri’a 104,009.

    Ya ce kuri'u 141,694 hadi da na Gama a karamar hukumar Nasarawa wadanda aka soke daga kananan hukumomi 22.

  14. Jihohi shida ne yanzu ba a kammala zabensu ba, Sakamakon zaben gwamnoni

    Yanzu jihohi shida ne ba a kammala zaben gwamna ba wadanda suka hada da Adamawa da Sokoto da Benue da Kano da Filato da Bauchi

  15. INEC ta ce ba a kammala zaben Kano ba, Sakamakon zaben gwamnan Kano

    Babban jami'in tattara sakamako zabe a Kano Farfesa B.B Shehu ne ya sanar da cewa ba a kammala zabe a Kano ba.

    A cewarsa Abba Kabir Yusuf na babbar jam’iyyar hamayya PDP ya samu kuri’a 1,014,474 yayin da gwamna mai ci na Jam’iyyar APC Abdullahi Umar Ganduje ya samu kuri’a 987,819.

    Jam’iyyar PRP ce ta zo a matsayi na uku da kuri’a 104,009.

    Ya ce kuri'u 141,694 hadi da na Gama a karamar hukumar Nassarawa wadanda aka soke daga kananan hukumomi 22.

  16. Ana bayyana sakamakon zaben gwamnan Kano, Sakamakon zaben gwamnan Kano

  17. Ganduje ya yi kira ga magoya bayansa, Sakamakon zaben gwamnan Kano

    Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje dan takarar jam'iyyar APC ya yi kira ga magoya bayansa su kwantar da hankalinsu.

    Wannan na zuwa bayan bayyana sakamakon Nassarawa, karamar hukuma ta karshe da ta rage a kammala tattara sakamakon dukkanin kananan hukumomin jihar inda sakamakon ya nuna PDP mai hamayya ce kan gaba.

    Cikin wata sanarwa da mai takaimawa gwamnan kan kafofin sadarwa na Intanet Salihu Tanko Yakasai ya fitar ya ce suna kira ga magoya bayansu su jira sanarwar karshe daga bakin shugaban hukumar zabe na jiha.

    "Sakamakon karamar hukumar Nasarawa da aka kawo shi ne na karshe amma akwai sauran aiki,"

    Sai an hada lissafin abun da APC ta samu, da wanda PDP ta samu sannan a duba ratar da Jam'iyar mai rinjaye ta samu, sannan daga karshe a yi la'akari da yawan adadin kuri'un da aka soke zabensu, idan sun haura rinjayen da Jam'iyar da ke kan gaba ta samu to ya zama wajibi a sake zabe a guraren da aka soke zabe," in ji shi.

    Gwamna Ganduje

    Asalin hoton, Salihu Tanko Yakasai

  18. Kaduna ta kafa tarihi a arewa - El-Rufa'i, Sakamakon zaben gwamnan Kaduna

    Gwamnan Kaduna Malam Nasir Ahmad El-Rufai ya ce Kaduna ta kafa tarihi na zaben mace ta farko a matsayin mataimakiyar gwamna a yankin arewacin Najeriya.

    A cikin jawabinsa na amincewa da sake zabensa gwamnan Kaduna a wa'adin shugabanci na biyu, El-Rufai ya gode wa mutanen Kaduna da suka zake ba shi dama sannan kuma yadda suka amince suka zabi mataimakiyarsa mace.

    "Kun bijere wa wadanda ba su son ganin an ba mata dama domin nuna basirarsu," in ji shi.

    Ya kara da cewa Dr. Hadiza Sabuwa Balarabe za ta yi aiki tare da kokarin tabbatar da ci gaban jihar Kaduna.

    Batun daukar musulma a matsayin mataimakiyar gwamna El-Rufai ya janyo ce-ce-ku-ce tare da kara haifar da zafin siyasar kabilanci a Kaduna.

    El-Rufa'i ya doke dan takarar PDP Isa Ashiru wanda ya dauki Kirista a matsayin mataimaki.

  19. Matakin da INEC ta bi wajen fitar da sakamakon Nassarawa, Sakamakon zaben gwamnan Kano

    Hukumar zabe a Kano ta ce ta yi amfani ne da mazabu 10 kawai da ba a samu matsala ba a karamar hukumar Nassarawa bayan bangaren APC sun ce ba su yadda da zaben wasu mazabu ba.

    Hukumar ta sanar da sakamakon ne daga wanda ta samu daga runfuman zabe, bayan yaga sakamakon farko na karamar hukumar ta Nassarawa.

    Shugaban INEC a Kano Farfesa Riskuwa ya ce: "Mun tura ma'aikatanmu sun je sun yi aikin zabe sun dawo kamar yadda ya kamata, to idan aka samu matsala dokokinmu sun ba mu damar yin amfani da wasu hanyoyi na tattara sakamako da doka ta amince da su.

    "Don haka ina kalubalantar duk wadanda ke cikin dakin nan da su nuna inda INEC a Kano ta saba doka wajen tattara sakamakon.

    "Mu yi amfani da mazabu 10 kawai da babu matsala muka kyale saura," in ji shi.

    Sakamakon zaben Kano
    Bayanan hoto, PDP ta lashe zabe a Kano
  20. PDP ta lashe karamar hukumar Nasarawa

    Jam'iyyar PDP ta lashe zaben karamar hukumar Nasarawa inda ta samu kuri'u 54,349, yayin da jam'iyyar APC ta samu kuri'u 34,297 a cewar baturen zaben karamar hukumar.